Kasar New Zealand ta yi bankwana da 2020, tana bikin shiga shekarar 2021
- Kasar New Zealand na daya daga cikin kasashen duniya da suka riga suka shiga shekarar 2021 yayinda sauran kasashe ke jiran shiga sabuwar shekara
- Kasar ta bi sahun sauran kasashe irin su Tonga, Samoa, Kiribati/Christmas Island wajen bikin shiga sabuwar shekara
- Shekarar 2020 ta zo da tarin kalubale kuma mutane a fadin duniya na fatan samun sassauci a 2021
Yayinda duniya ke jiran shiga shekarar 2021 a wasu yan sa’o’i daga yanzu, tuni kasar New Zealand ta fara bikin sabuwar shekara da kayan alatu.
A wani bidiyo da shafin Bloomberg Quicktake ya wallafa a Twitter, an gano kasar ta cika da haske na alatu wanda ke nuni ga shiga sabuwar shekara yayinda mutane suka cika da farin cikin ganin sabuwar shekarar.
KU KARANTA KUMA: Manyan ayyuka 9 da ma'aikatar Pantami ta gudanar a shekarar 2020
Sauran kasashen da suka shiga 2021 sun hada da kananan kasashe irin Tonga, Samoa da Kiribati/Christmas Island.
Tuni mutane suka yi tururuwan zuwa shahin yin sharhi domin murnar shiga sabuwar shekara.
Mai amfani da shafin Twitter @SarahChamps3753 ta rubuta:
"Ina birnin Auckland tare da iyalina sai na hango wutan disko na tashi – Barka da shiga sabuwar shekara!"
@MichaelNotABot8 ya wallafa:
"Ina kishi. Yanzun nan na fara ranar 31 ga watan Disamba.”
KU KARANTA KUMA: Cikakken sunayen shahararrun masu mukaman siyasa 5 da Buhari ya sallama a 2020
A wani labarin kuma, mun ji cewa iyalan Suleiman Olufemi, wani dan Najeriya da ke cikin jerin wadanda aka yankewa hukuncin kisa a Saudiyya tsawon shekaru 18, sun roki gwamnatin tarayya da ta kawo dauki don ceto mutumin.
Shugabar kungiyar yan Najeriya mazauna kasar waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana hakan.
A cewar Dabiri-Erewa, iyalan sun ziyarci NIDCOM don rokon afuwa kan Suleiman wanda aka yanke wa hukuncin kisa shekaru 18 da suka wuce.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng