Masu garkuwa sun saki uwa da yarta, sun rike mijin a Anambra

Masu garkuwa sun saki uwa da yarta, sun rike mijin a Anambra

-Yan bindiga sun ci gaba da rike miji bayan sun yi garkuwa da shi da iyalan sa a titin Enugu-Agidi-Nawgu a jihar Anambra

- Shugaban yankin Enugu-Agidi ya bayyana damuwar sa game da batun garkuwa da mutane a yankin inda yace wannan ne karo na biyu cikin wannan shekarar

- Ya sake bayyana cewa akwai bukatar yawaitar jami'an tsaro da kuma gyara titin don yin tuki cikin kwanciyar hankali

Masu garkuwa da mutane, ranar Talata, sun yi garkuwa wasu ma'aurata da yarsu a titin Enugu-Agidi-Nawgu a karamar hukumar Dunukofia da ke jihar Anambra.

Shugaban yankin Enugu-Agidi, Ndubuisi Obijiofor, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Laraba, The Punch ta ruwaito.

Ya ce an kwashe wanda aka yi garkuwar da su zuwa daji bayan yan bindigar sun yi harbe harbe.

Masu garkuwa sun saki uwa da yarta, sun rike mijin a Anambra
Masu garkuwa sun saki uwa da yarta, sun rike mijin a Anambra. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ba don cin mutuncin Jonathan na nada Sanusi Sarkin Kano ba, in ji Kwankwaso

Obijiofor ya ce sun tuntubi yan sanda, wanda a take suka fara kokarin ceto wanda aka yi garkuwar da su.

Ya ce an saki matar da yarta da misalin karfe 3:00 na daren Laraba, amma ba a saki mijin ba.

Obijiofor ya shaida cewa, "wannan ne karo na biyu da yan bindiga suka yi garkuwa da mutane a wannan titin cikin wannan shekarar, kuma karo na hudu cikin shekara biyu.

"Lamarin garkuwa da mutane a titin Enugu-Agidi-Nawgu ya zama abin damuwa; akwai bukatar karuwar jami'an tsaro da kuma gyara titin don tuki cikin lumana."

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin.

KU KARANTA: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle

Ya ce sun samu kiran waya daga yankin da abin ya faru kuma an tura jami'an gaggawa zuwa inda abin ya faru.

"Bazan iya tabbatar da cewa garkuwa da mutane bane saboda bamu samu rahoton da ke tabbatar da hakan ga yan sanda ba," inji Mohammed.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel