Ba don cin mutuncin Jonathan na nada Sanusi Sarkin Kano ba, in ji Kwankwaso

Ba don cin mutuncin Jonathan na nada Sanusi Sarkin Kano ba, in ji Kwankwaso

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje martani kan batun nada Sanusi II sarkin Kano

- Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya nada Sanusi sarki ne domin cin zarafin Goodluck Jonathan

- Kwankwaso ya ce ya bi doka wurin nada Sanusi II kuma ya zabe shi ne don ya fi sauran maneman ilimin addini da boko, ya kuma fi karbuwa wurin al'umma

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi'u Kwankwaso ya musanta zargin nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano don cin zarafin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Ya yi wannan jawabi ne yana mai mayar da martani ga zargin da Gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje ya yi masa, The Nation ta ruwaito.

Ba don ci wa Jonathan fuska na nada Sanusi Sarkin Kano ba, Kwankwaso
Ba don ci wa Jonathan fuska na nada Sanusi Sarkin Kano ba, Kwankwaso. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle

Ganduje ya yi wannan zargin ne a wurin bikin kaddamar da wata littafi. Ya kuma kara da cewar ko lokacin da a ka nada Sanusi a 2014, ba shi ne mafi cancanta ba. Ya kuma ce an tsige Sanusi ne don kare martabar masarautar .

Sai kuma ga shi Kwankwaso ya fito ya musanta hakan ya na mai cewar an bi ka'idar masarautar Kano yadda ya kamata wurin nadin Sanusi.

KU KARANTA: Dakarun soji sun kama gagarumin bokan Gana da 'yan kungiyarsa

Ya ce Sanusi ya fi sauran maneman ilimin Boko da Addini kuma ya fi su karbuwa wurin jama'a.

"Matsuwar da Gwamna Ganduje ya yi na neman ciwo bashin dala biliyan 1.8 da kuma Allah wadai da Sanusi ya yi game da hakan shi ne dalilin tsige shi.

"Kowa ya san Sanusi ya fi Ganduje wayewa wanda wannan shi ne dalilin tsige shi da kuma kacaccala masarautar da kuma nada Sarakunan da za su biyema son ransa," In ji Kwanjwaso ta bakin babban sakatarensa.

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164