Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle
- Gwamna Bello Muhammad Matawalle na Jihar Zamfara ya bayyana hanya guda da za a bi don kawo karshen 'yan bindiga a Najeriya
- Gwamnan ya ce Zamfara ne cibiyar 'yan bindiga a Arewa don haka ya zama dole a binciko dukkan sansanin 'yan bindiga da ke jihar a lalata su
- Matawalle ya yi kira ga sauran takwarorinsa na jihohin Arewa da hukumomin tsaro su mayar da hankali a Zamfara domin samun nasara a kan yan bindigan
Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ce lalata dukkanin sansanin 'yan bindiga da ke Jihar Zamfara ne zai kawo karshen hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa a Arewa maso Yammacin kasar.
Matawalle ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke ganawa da Kwamitin Ayyuka na kasa na jam'iyyar PDP da suka kai masa ziyara karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar na kasa Prince Uche Secondus don masa jajen rasuwar mutum 8 cikin tawagar Sarkin Kauran Namoda da 'yan bindiga suka kashe.
DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda
Ya ce za a ci galaba a kan 'yan bindigan idan dukkan gwamnonin yankin sun hada kai wuri guda domin a lalata sansanin 'yan bindigan da ke Jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
"Zamfara ce cibiyar 'yan bindiga a Arewa kuma idan an dauki matakin da ya dace a kan 'yan bindiga a Zamfara, ina tabbatar maka cewa batun hare-haren 'yan bindiga a Arewa zai zo karshe.
"Don haka ina kira ga takwarori na da hukumomin tsaro su saka ido a Jihar Zamfara domin mu gano dukkan sansanin 'yan bindigan mu lalata su.
KU KARANTA: Dakarun soji sun kama gagarumin bokan Gana da 'yan kungiyarsa
"Idan ba mu lalata sansanin su ba, ba dole bane mu iya kawo karshen 'yan bindiga a Arewa ko Najeriya. Duk abinda 'yan bindiga za su fada maka yayin sulhu, ya zama dole mu kwace dukkan makaman da ke hannunsu, idan ba muyi hakan ba, ba zamu cimma burinmu ba," in ji shi.
A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.
Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.
Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng