Rashin tsaro: Jibwis ta umurci limamai su fara Al Ƙunuti yayin salloli

Rashin tsaro: Jibwis ta umurci limamai su fara Al Ƙunuti yayin salloli

- Kungiyar Izala ta Jibwis ta bukaci dukkan limamai da su fara yin Al kunuti yayin salloli biyar na kowanne rana don samun zaman lafiya

- Shugaban kungiyar, Sheikh Bala Lau ne ya bada wannan sanarwar da aka watsa ta kafafen dandalin sada zumunta na kungiyar

- Tun a makon data gabata wasu masallatan Juma'a sun fara addu'o'in na musamman don samun zaman lafiya a kasar

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatul Bidia Waikamatussunnah, JIBWIS, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya umurci dukkan malamai da ke limancin khamsul-salawat su fara yin Al kunuti a yayin salolin domin neman Allah ya kawo saukin rashin tsaro a kasar.

Shugaban ya yi wannan kirar ne ta hanyar amfani da shafukan dandalin sada zumunta na kungiyar ta JIBWIS a ranar Talata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rashin tsaro: Jibwis ta umurci limamai su fara Al Kunuti yayin salloli
Rashin tsaro: Jibwis ta umurci limamai su fara Al Kunuti yayin salloli. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Idan Boko Haram sun gama da Arewa, za su tunkari Kudu, Aisha Yesufu

Ya yi kira ga al'umma su tuba daga zunuban da suke aikatawa su kuma nemi gafarar Ubangiji duba da yadda lamarin rashin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar.

"Shugaban kungiyar Jibwis ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya umurci dukkan malaman addinin musulunci musamman wadanda ke limancin sallah su fara yin Al kunuti don neman taimakon Allah bisa halin rashin tsaro," a cewar sanarwar.

KU KARANTA: Waiwaye: Manyan nasarori uku da Shugaba Buhari ya samu tun hawansa mulki

Idan za a iya tunawa, masallatan Juma'a sun fara Al kunutin tun a makon data gabata da nufin Allah ya kawo zaman lafiya da tsaro a kasar musamman yankin arewa inda abin ya fi kamari.

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel