Idan Boko Haram sun gama da Arewa, za su tunkari Kudu, Aisha Yesufu
- Aisha Yesufu, yar gwagwarmaya mai zanga zange sanye da hijabi ta ce Boko Haram za su afka Kudancin Najeriya
- Aisha ta ce da zarar 'yan ta'addan sun gama da yankin Arewa za su fuskanci kudancin kasar su hana su sukuni
- Don haka ta shawarci yan Najeriya daga dukkan yankuna su hada kansu su nemo hanyoyin magance matsalar don ba a yanki daya abin zai tsaya ba
Yar gwagwarmaya kuma daya daga cikin wadanda suka hada zanga zangar Bring Back Our Girls (BBOG) ta yi hasashen cewa 'yan ta'addan Boko Haram za su ratsa jihohin Kudancin Najeriya idan sun gama da Arewa.
Ta yi wannan jawabin ne bayan harin da 'yan ta'addan suka kai a makarantar sakandare ta Kankara da ke Jihar Katsina da daga bisani kungiyar ta yi ikirarin cewa ita ta kai harin.
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari
Ta ce, "Idan Boko Haram ta gama da Arewa, zata fuskanci Kudancin kasar. Idan kana tunanin bai shafe ka ba, wasu ma a baya sunyi tunanin bai shafe su a lokacin da abinda ke faruwa a arewa maso gabas amma yanzu sun ga yadda ta kasance.
A cewar Aisha, ya kamata 'yan Najeriya su yi takatsantsan inda ta ce, "Duk wani harin ta'addancin da aka kai wa wani a ko ina ya shafe mu baki daya."
KU KARANTA: Jihohi 10 da suka fi dogara da kasafin wata-wata na gwamnatin tarayya
A bangarenta, kungiyar Kirista ta Najeriya ta yi kira ga gwamnati ta rufe dukkan makarantun kwana a arewacin Najeriya.
Ta kuma bukaci a umurci jami'an hukumar tsaro ta NSCDC su tsare dukkan makarantu da ake ganin suna cikin hatsari.
A wani labarin, rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami'anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na 'yan sanda mafi kusa.
The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja. Rundunar soji tana neman jami'anta 43 ruwa a jallo.
Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami'an rundunar da ke da bayannan game da jami'an da suka tsere su kamo su 'idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu'.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng