An kuɓutar da uku daga cikin ƴan sanda huɗu da ɓarayin mutane suka ƙwamushe

An kuɓutar da uku daga cikin ƴan sanda huɗu da ɓarayin mutane suka ƙwamushe

- Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa ta samu nasarar kubutar da wasu jami'anta guda uku da aka sace

- Wasu 'yan bindiga da ake zargin ma su garkuwa da mutane ne suka kai hari a kan tawagar 'yan sanda bayan sun kamo ma su laifi

- 'Yan bindigar sun saki ma su laifin da aka kamo sannan sun yi awon gaba da jami'an rundunar 'yan sanda guda hudu

An samu nasarar ceto uku daga cikin jami'an ƴan sanda da wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ma su garkuwa da mutane ne suka sace, kamar yadda Premium Times ta raito.

Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta sanar da cewa ta ceto uku daga cikin jami'an ta huɗu da ƴan ta'adda su ka sace a unguwar Tuntun dake Ijebu Igbo a ƙaramar hukumar Ijebu North ta jihar Ogun.

Kakakin Rundunar ƴan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, shine ya bada sanarwar lokacin zantawa da manema labarai a babban birnin jihar Ogun, Abeokuta, a ranar Asabar.

KARANTA: Sati guda bayan kisan manoma 43, mayakan Boko Haram sun kai sabon hari Banki

Sai dai, Oyeyemi ya ce har yanzu akwai jami'insu guda ɗaya mai muƙamin constable da ke riƙe a hannu ƴan ta'addar.

An kuɓutar da uku daga cikin ƴan sanda huɗu da ɓarayin mutane suka ƙwamushe
An kuɓutar da uku daga cikin ƴan sanda huɗu da ɓarayin mutane suka ƙwamushe
Asali: UGC

Sai dai kakakin ya ce tuni yan sanda suka baza komarsu a yankin don ceto jami'in na su guda daya da ya rage.

Ya ce, "a halin yanzu rundunar ta cafke mutum uku waɗanda ake zargi da hannu dumu dumu a ƙwamushen, kuma suna taimakawa ƴan sanda wajen gudanar da bincike".

KARANTA: Kokarinku ya yi kadan, ba zan kara karbar uzuri ba; Buhari ya kwankwashi su Buratai

A cewar yallaɓai Oyeyemi, "mai garin ƙauyen ya turowa da ƴan sanda ƙorafin akwai ɓatagari masu ɗauke da muggan makamai a ƙauyensa.

"Ba tare da wata wata ba, DPO na yankin ya jagoranci tawagar jami'ai tare da ƴan kungiyar sa kai, inda suka kai samame tare"

"An yi nasarar samun bindigu 16 masu bututu, sai bindigu masu sunduƙi 16 (Dane guns), da fakitin alburusai guda 16 tare da kama waɗanda ake zargin.

"A ƙoƙarin kai waɗanda ake zargin caji ofis, sai wasu ƴan ta'adda suka kai farmaki kan jami'an ƴansanda inda suka ƙwamushe huɗu daga cikin su."

"Nan suka harbi DPO a kafaɗa, inda suka saki waɗanda ake zargin."

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, an dawo da wani tsohon bidiyo da shugaba Buhari ke zargin gwamnatin tarayya da zama babbar mai daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke takara, gabanin zaben shekarar 2015.

Dawo da bidiyon tamkar tuni ne ga shugaba Buhari domin ya tuna alakwuran da ya daukarwa 'yan Najeriya yayin yakin neman zabe.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel