Idan hagu ta ki, sai a koma dama: Gwamna Sule na APC ya bawa Buhari muhimmiyar shawara a an tsaro
- Abdullahi Sule, gwamna mai ci a jam'yyar APC, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a sauya salo da dabara wajen yaki da ta'addanci
- Gwamnan ya bayyana hakan ne a matsayin shawara ga shugaba Buhari yayin da ya ziyaci Maiduguri
- A ranar Asabar ne gwamna Sule tawagar gwamnatin jihar Nasawa domin yi wa gwamna Zulum ta'aziyya
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan ya sauya salo tare da gwada wasu sabbin hanyoyin yaki da ta'addanci, musamman domin kawo karshen matsalar Boko Haram, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
A cewar Sule, akwai bukatar sauya salon yaki da kungiyar Boko Haramm da sauran ayyukan ta'addanci a sassan kasa, saboda hanyar da ake amfani da ita wajen magance matsalar ta ki kai wa ga nasara
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci wakilcin gwamnatin jihar Nasarawa zuwa Maiduguri domin yi wa gwamna jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ta'aziyar kisan manoma 43 da 'yan Boko Haram su ka yi.
KARANTA: Farfesa Yusuf Usman: 'Yan bindiga suna da layukan wayar gwamnonin Arewa
A cewar gwamnan, "tunda mun yi amfani da wasu hanyoyi domin samun galabar matsalar amma hakan ba ta samu ba, tamkar manuniya ce a kan cewa lokacin fara sabon tununi ya yi, musamman ganin cewa an gwada hanyoyi da dama, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba hakan bai warware balle ya kawo karshen matsalar ba."
KARANTA: Kokarinku ya yi kadan, ba zan kara karbar uzuri ba; Buhari ya kwankwashi su Buratai
Ya karfafa cewa babu wata matsala idan an yi tunanin sauya dabara da salo domin a kawao karshen matsalar, kowa ya huta, a zauna lafiya.
A baya Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa babban hafsan rundunar soji, Janar Tukur Buratai, ya gargadi anyan sojoji a kan juyin mulki.
Buratai ya ce dimokradiyya ta zo kenan, zama daram, a saboda haka lokacin katsalandan daga wurin sojoji ya wuce.
Buratai ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin da ya ke gabatar da jawabi bayan ya kammala daura damarar kara girma ga sabbin manyan sojoji 39 da aka karawa girma zuwa mukamin manjo janar.
Babban hafasan rundunar sojin ya bayyana hakan ne yayin bikin karin girma ga wasu manyan sojoji 39 zuwa mukamin manjo janar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng