Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari Banki a jihar Borno

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari Banki a jihar Borno

- A yayin da har yanzu ba'a daina kisan manoma 43 ba, 'yan Boko Haram sun sake kai hari Banki a jihar Borno

- Garin Banki ya kasance daya daga cikin wuraren da kungiyar Boko Haram ke son cimma saboda cibiya ce ta ayyukan kungiyoyin jin kai

- Rahoton da Legit.ng ta samu ya nuna cewa dakarun rundunar soji sun dakile harin da mayakan su ka kai

An fafata a tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da dakarun soji a Banki, wani gari da ke kan iayakar kasar Kamaru da Najeriya.

Jaridar HumAngle ta rawaito cewa dakarun rundunar soji sun samu nasarar dakile harin da aka kai garin Banki da ke karkashin karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Garin Banki, mai nisan kilomita uku kacal daga iyakar Najeriya da kasar Kamaru, ya kasance cibiyar ayyukan kungiyoyin jin kai.

KARANTA: Kokarinku ya yi kadan, ba zan kara karbar uzuri ba; Buhari ya kwankwashi su Buratai

A cikin watan Nuwamba ne Amina Mohammed, mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya (UN), ta ziyarci wani sansanin 'yan gudun hijira da kuma wasu 'yan Najeriya daga kasar Kamaru.

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari Banki a jihar Borno
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari Banki a jihar Borno @Thecable
Source: Twitter

Duk da haka, Banki na daga cikin yankunan da kungiyar Boko Haram, musamman mai biyayya ga ISWAP, keda karfi.

Kungiyar Boko Haram ta taba kai hari tare da dakatar da ayyukan jin kai a Banki sakamakon wani mummunan hari da ta yankin a watan Nuwamba na shekarar 2019.

KARANTA: Matsalar Tsaron Najeriya ta fi ƙarfin Soja, in ji Gwamnono

Legit.ng hausa ta rawaito gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, na shawartar shugaba Buhari, a kan ya sauya salo tare da gwada wasu sabbin hanyoyin yaki da ta'addanci, musamman domin kawo karshen matsalar Boko Haram.

A cewar Sule, akwai bukatar sauya salon yaki da kungiyar Boko Haramm da sauran ayyukan ta'addanci a sassan kasa, saboda hanyar da ake amfani da ita wajen magance matsalar ta ki kai wa ga nasara

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci wakilcin gwamnatin jihar Nasarawa zuwa Maiduguri domin yi wa gwamna jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ta'aziyar kisan manoma 43 da 'yan Boko Haram su ka yi.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel