Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi

Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi

- An tsananta tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke Yenagoa saboda gudun 'yan ta'adda

- A ranar Alhamis da ta gabata ne 'yan ta'adda dauke da makamai suka afka wa kotun, inda suka fatattaki lauyoyi

- Sun yi kaca-kaca da duk wasu takardu da abubuwan amfanin kotun, sun kuma sace kudade da wayoyi

An tsananta tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke Yenagoa, jihar Bayelsa a ranar Juma'a don gudun kutsawar 'yan ta'adda kamar yadda suka yi a ranar Alhamis da rana.

'Yan ta'addan da ke dauke da miyagun makamai, wadanda yawansu ya kai 20, inda suka fi karfin jami'an tsaro kuma suka kutsa cikin kotu mai daraja ta II, wacce take kula da tsayar da 'yan takarar jam'iyyar APC da na PDP a Bayelsa ta tsakiya.

Sun lalata duk wasu abubuwa masu muhimmanci na ofishin da ake ajiye kayan shari'ar da kuma kayan amfanin kotun, Vanguard ta wallafa.

'Yan ta'addan sun fatattaki lauyoyi da ma'aikatan kotun, sannan sun kwashe kudade, wayoyi da sauran abubuwa masu daraja.

KU KARANTA: Ku dakatar da dukkan burikanku na 2023, Saraki ya shawarci 'yan siyasa

Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi
Gagarumin rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Allah ba zai bar ka ba idan ka siya wa matarka mota, ka bar mahaifiyarka tana yawo a kasa, Mawaki

A wani labari na daban, shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce sai an zage damtse kafin a samu nasarar yaki da 'yan ta'adda a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

A jiya ne Tinubu ya nuna matsananciyar damuwarsa a kan yadda 'yan Boko Haram suka yi wa manoma 43 na jihar Borno kisan wulakanci.

Manoman da basu ji ba basu gani ba, sun mayar da hankulansu wurin nema wa iyalansu abinci, amma rashin tsaro ya janyo musu bala'i.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng