'Yan daba dauke da makamai sun tare Sanatan APC, sun bukaci N2m a take

'Yan daba dauke da makamai sun tare Sanatan APC, sun bukaci N2m a take

- Wani dan ta'adda ya tunkari sanata Elisha Abbo na jihar Adamawa da bindigar toka

- Ya yi yunkurin harbinsa matsawar bai bashi Naira miliyan 2 ba, jami'an tsaro kuwa suka damke shi

- Sanatan ya ce talauci da rashin aikin yi ne suka addabi matasa, zai taimaka musu da abin dogaro

Ishaku Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa ya tsallake rijiya da baya.

Kamar yadda Legit.ng ta ga wata takarda wacce tazo daga ofishin yada labaran sanatan, wani mutum mai dauke da bindigar toka ya lallabo ya tare shi, inda yayi barazanar harbinsa matsawar bai bashi miliyan 2 ba.

Takardar, wacce hadimin sanatan a kan harkokin yada labarai, Michael Volgent ya saka hannu, ya ce al'amarin ya faru ne da misalin 2pm, inda matasa da yawa suka tare hanyar, yana hanyarsa ta zuwa bikin dan uwansa da ke Mubi.

'Yan daba dauke da makamai sun tare Sanatan APC, sun bukaci N2m a take
'Yan daba dauke da makamai sun tare Sanatan APC, sun bukaci N2m a take. Hoto daga Senator Elisha Abbo
Source: Facebook

KU KARANTA: Allah ba zai bar ka ba idan ka siya wa matarka mota, ka bar mahaifiyarka tana yawo a kasa, Mawaki

Kowa ya san sanata Abbo a matsayinsa na mutum mai taimako.

A cewarsa, wannan yunkurin hallaka sanatan ne, saboda mutumin yana rike da bindiga tsirararta. Ba kamar yadda bidiyoyi suke yawo a kafafen sada zumuntar zamani ba, wadanda suke nuna 'yan siyasa suna ganganci da rayuwar mutane.

Tuni aka damka wa hukuma mutumin bayan faruwar lamarin, don a cigaba da bincike a kansa.

Sanata Abbo ya daura laifin akan fatara da rashin aikin yi a matsayin dalilan da suke sanya matasa yin ta'addanci. Ya lashi takobin yin wani abu a kai, dama shi mutum ne mai taimako.

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya ta matukar girgiza da kalubalen tsaro, Gwamnoni

A cewarsa: "Matasa suna shiga cikin harkar ta'addanci, har su kai ga lalata rayuwarsu, sannan su gurbata unguwanni gaba daya.

"Ba da gangan ya kawo min farmaki ba, talauci da rashin aikin yi ne suka tunzura shi har ya aikata hakan. Zan yi iyakar kokarina wurin ganin na tsamosu daga cikin wannan mawuyacin halin."

A wani labari na daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bukaci gwamnati ta bai wa mata damar shiga harkar mulki, don a dama dasu. A cewarsa, gwamnatinsa ta bai wa mata dama a matsayi daban-daban.

Gwamnan ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 2 ga watan Disamba, yayin tattaunawa da NGWA-GBV a Abuja.

A wata takarda wacce wakilin Legit.ng ya gani, inda kakakin gwamnan, Onogwu Mohammed, ya gabatar wa da manema labarai, wacce gwamnan yace ya aiwatar da duk abubuwan da yake shawartar sauran gwamnoni su yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel