Hotunan ranar daurin auren jarumi Nuhu Abdullahi da zukekiyar amaryarsa
- Jarumin masana'antar Kannywoood Nuhu Abdullahi, ya angwance da zukekiyar amaryarsa
- Jarumin ya wallafa kyawawan hotunansa da sabuwar amaryarsa a shafinsa na Instagram
- Ya kara da wallafa hotunan wurin daurin aure tare da abokai, 'yan uwa da abokan sana'arsa
Fitaccen jarumin masana'antar fina-finan hausa, Nuhu Abdullahi, ya angwance da kyakyawar amaryarsa Siyama.
An daura auren kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a ranar Juma'a, 4 ga watan Disamban 2020.
Kafin ranar aduarin auren, an fara ganin hotunan jarumin tare da kyakyawar amaryarsa na kafin aure suna yawo a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.
KU KARANTA: Bola Tinubu ya bada shawarar yadda za a kawo karshen ta'addanci a kasar nan
Jaruman masana'antar tare da masoyan jarumin sun dinga masa kyawawan addu'o'i tare da fatan alheri.
A ranar Alhamis sai ga hotunan shagalin kamun auren da aka yi tare da kyakyawar amaryarsa.
Bayan daurin auren da aka yi a masallacin Juma'a na Alfurqan da ke Alu Avenue a GRA Nasarawa da ke jihar Kano, an ga hotunan jarumin da 'yan uwa tare da abokan arziki.
Ya wallafa hotunan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Instagram inda aka ga jarumi Ibrahim Maishunku tare da Malam Aminu Saira a wurin daurin aure.
KU KARANTA: Babban laifi ne cigaba da ajiye hafsoshin tsaro, Shekarau ya kalubalanci Buhari
A wani labari na daban, a ranar Alhamis, sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana yadda shugabannin tsaro suka dade a kan kujerunsu, inda yace ya kamata su tafi gida su huta, Daily Trust ta wallafa.
Kiraye-kiraye don cire shugabannin tsaro ya fara yawa ne tun bayan ganin yadda harkokin tsaro suka tabarbare.
Sanatan ya roki fadar shugaban kasa, inda ya bukaci a sauya su da wasu, bayan kashe-kashen manoman shinkafa na Zabarmari a jihar Borno.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng