Saurayi ya biya wa budurwa 432,000 a mashaya, ta ki sauraronsa kuma ta bi wani saurayi

Saurayi ya biya wa budurwa 432,000 a mashaya, ta ki sauraronsa kuma ta bi wani saurayi

- Wani saurayi ya kwashe duk kudaden da ke asusunsa na banki don biyan kudin da wata budurwa ta kashe Naira dubu 432 a mashaya

- Saurayin ya wallafa wannan al'amarin da ya faru dashi a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya nuna takaicin faruwar lamarin

- A cewarsa, ko saurararsa ba ta yi ba bayan ya amince da biyan kudin, tace wani saurayinta na wajen mashayar yana jiransu

Wani mutum mai suna London Akan, ya bayyana yadda ya tatike asusun bankinsa wurin biyawa wata budurwa Naira 432,000 da ta kashe a wata mashaya.

Kamar yadda yace, ya hango wata kyakkyawar budurwa mai sura, zaune tare da kawayenta a mashayar, The Nation ta wallafa.

Don ya samu gurbi a zuciyarta, sai ya yanke shawarar biyan duk kudaden da budurwar da kawayenta suka kashe, kwatsam aka sanar dashi sun kashe Naira 432,000.

Kamar yadda ya wallafa, "Na hango wata budurwa tare da kawayenta, nayi ta tunanin yadda zan tunkareta, sai na yanke shawarar biyan duk kudaden da suka kashe. Sai na samu ma'aikacin mashayar nace ya sanar da budurwar cewa zan biya kudaden.

"Ma'aikacin yaje yayi musu magana, sai suka yi murmushi suka dago min hannu. Sun tashi za su tafi sai na nufi inda suke, nace ina so inyi magana da budurwar kafin su tafi. Kawai sai tace min akwai wani saurayinta da ke jiransu waje. A haka suka yi gaba suka kyaleni.

"Bayan na juya wurin tambayar kudin ne, aka sanar dani cewa Naira 432,500 ne. A nan ne jikina ya dauki rawa, nake tambayar ta ina kudinsu zai zama 432,500?

"Sai yace min ai sun siya abubuwa da dama a wurin, kuma wanda suka zo tare da su ya bayar da wani kati da za su biya kudin dashi, amma tunda zaka biya sun tafi dashi.

"Sai na tambayi idan za'a iya rage min kudin, suka ce ai a haka an rage, don asalin kudin Naira dubu 490 ne. A haka na cire duk kudin asusuna na banki na biya, ban iya shan komai ba a wurin sai Shisha."

KU KARANTA: Ku zabge kudin makaranta ko a soke zango na 3 na karatu - Gwamnatin Kano ga masu makarantun kudi

Budurwa ta talauta ni yayin da nayi yunkurin biya mata siyayyarta - Saurayi
Budurwa ta talauta ni yayin da nayi yunkurin biya mata siyayyarta - Saurayi. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hukumar Hisbah da KAROTA za su fara kama masu batsa wurin siyar da magungunan gargajiya

A wani labari na daban, wani zakaran kokuwa yayi ajalin wani dan sandan Philippine da wukar dake makale a kafarsa, a cewar wasu jami'ai ranar Laraba, jaridar The Nation ta wallafa haka.

An hanzarta da Christian Bolok, shugaban 'yan sandan garin San Jose da ke arewacin Samar, asibiti bayan faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya mutu take-yanke.

Ya jagoranci 'yan sanda wurin dakatar da gasar damben zakaru a wani kauye da ke San Jose, inda ya dauki daya daga cikin zakarun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng