Sabon sarkin Zazzau: Na shiga littafi na uku kuma na karshe, inji El-Rufai

Sabon sarkin Zazzau: Na shiga littafi na uku kuma na karshe, inji El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ya shiga littafi na uku kan tsarin zabar sabon sarki Zazzau

- Tun farko dai ya ce yana karance-karance ne domin su zame masa ja-gaba wajen fahimtar yadda zai bullowa batun nada sabon sarkin

- El-Rufai ya kuma bukaci jama'a da su ci gaba da taya shi addu'a domin yin zabe nagari

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya sake yin karin haske kan halin da ake ciki game da zabar sabon sarkin Zazzau.

El-Rufai ya bayyana cewa a yanzu ya shiga cikin littafi na uku na karance-karancen yadda zai nada sabon sarki.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a daren ranar Asabar, 26 ga watan Satumba.

Ya kuma jaddada cewa wannan ne littafi na karshe da zai karanta kafin ya waiwayi rahoton ma’aikatar harkokin masarautu na jihar bayan tantance sunaye 11 da aka mika mata.

Sabon sarkin Zazzau: Na shiga na littafi na uku kuma na karshe, inji El-Rufai
Sabon sarkin Zazzau: Na shiga na littafi na uku kuma na karshe, inji El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Harin zaben 2023: Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP ya gana da Babangida a Minna

Gwamnan ya kuma roki jama’a da su ci aba da taya shi addu’ar Allah yayi masa jagora wajen zaba wa al’umman Zazzau sarkin da zai kawo cigabansu da masarautar Zazzau.

“Karin bayani kan Kaduna: Yayinda nake jiran rahoton ma’aikatar harkokin masarautu na jihar, ina cikin littafi na uku kuma na karshe kan tsarin zaben sabon sarki. Za a turo mani shawarwarin ma’aikatar da tsaro kan yan takarar domin yanke hukuncin karshe.

“Littafin Dr Hamid Bobboyi kan manufofin shugabanci bisa ga tsarin magabata na masarautar Sokoto yana tattare da nasarori masu yawa.

”Ina rokonku ku tayi da addu’a Allah ya yayi min jagora in zaba wa mutane sarki wanda zai dau saiti da cigaban zamani na wannan karni ta 2021 domin cigaban al’umma da masarautar Zazzau.”

KU KARANTA KUMA: Ba ruwan Buhari: Bashir Ahmad ya magantu kan zargin amfani da jirgin FG a shagalin bikinsa

A gefe guda, mun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ba za ta yi amfani da rahoton da majalisar nadin sarki na masarautar Zazzau ta kai mata ba domin cike gurbin sarkin Zazzau, wata majiya da ta san kan lamrin ta tabbatar wa da Premium Times.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel