Katsina: Hon. Fatihu ya yi wa Talakansa barazanar bada umarnin ayi masa duka

Katsina: Hon. Fatihu ya yi wa Talakansa barazanar bada umarnin ayi masa duka

- Fatihu Muhammad ya fadawa wani Bawan Allah cewa zai sa a yi masa duka

- ‘Dan Majalisar mai wakiltar yankin Daura ya bayyana haka ne a wayar tarho

Fatihu Muhammad, mai wakiltar yankin Daura, Sandamu, da Maiadua a majalisar wakilai, ya yi barazanar yi wa wani talakansa dukan tsiya.

A wani faifen sauti da yanzu ya ke ta yawo, an ji Honarabul Fatihu Muhammad ya na yi wa wani Malam Abdulbasid Bello Mai’adua barazana.

Jaridar Katsina Post ta ce wannan ‘dan majalisa ya kira Abdulbasid Bello Mai’adua a wayar tarho, inda ya fada masa cewa zai sa a ba shi kashi.

‘Dan siyasar ya shaidawa wannan Bawan Allah cewa idan har bai daina rubutu a game da shi a kan shafinsa na Facebook ba, zai yi maganinsa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari bai da hannu a shiga takara ta - Fatihu

A wannan faifai, an ji ‘dan majalisar ya na fadawa Malam Abdulbasid Bello Mai’adua cewa ya tafi ya kai shi kara gaban duk wanda ya ga dama.

Za a ji ‘dan majalisar na Daura da kewaye ya na cewa: “Ina so ka dauki wannan wayar da mu ke yi. Ina jan kunnenka cewa ka da nemi fada na.”

Honarabul Muhammad ya cigaba da cewa: “Domin ni ba sa’anka ba ne, kuma ba mai gidanka ba. Idan b aka rabu da ni ba, zan sa ayi maka duka.”

“Idan ka ga dama ka kai kara gaban duk wanda ka ga dama a jihar Katsina ko ma Najeriya.”

‘Dan majalisar tarayyar bai tsaya nan ba, ya cigaba da cewa: “Da alama kai jahili ne wanda bai san komai ba, bai san sha’anin cigaba ba.”

KU KARANTA: Bidiyon wata ganawar Shehu Idris ta Aminu Ado Bayero kafin ya rasu

Hon. Muhammad ya kira Malam Abdulbasid Bello Mai’adua wanda ya ke wakilta da jahilin da bai je makaranta ba, kuma maras kishin kasa.

“Idan ba ka fita harka ta ba, zan sa ayi maka duka a Mai’adua.” Inji ‘dan majalisar na APC.

Abdulbasid Bello Mai’adua ya tabbatarwa Katsina Post cewa babu shakka sun yi wannan wayar da ‘dan majalisarsa, kuma har an aiko masa ‘yan daba.

Mai’adua ya na zargin cewa ‘dan majalisar ne ya turo masa tsagera a Daura, ya ce bai taba kama sunan ‘dan siyasar a duk magangunun da ya ke yi ba.

A lokacin da aka fito da Fatihu Muhammad takara, kun ji cewa wasu mutane a Yankin Daura da Mai’Adua da kuma Sandamu sun yi zanga-zanga.

Jama’a sun koka cewa za a kakaba masu ‘Dan uwan Shugaban Kasa Buhari da karfi da yaji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel