Mala Buni: An fara cin ma nasara bayan mun gana da Tinubu da Akande

Mala Buni: An fara cin ma nasara bayan mun gana da Tinubu da Akande

- Mai Mala Buni ya yi magana game da zaman da su ka yi da Bola Tinubu

- Shugaban rikon kwaryar APC ya ce ganawar su ta kai ga kawo nasarori

- Shugabannin rikon APC sun yi zama da Tinubu da Bisi Akande kwanaki

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni kuma shugaban jam’iyyar APC na rikon-kwarya, ya yi magana da yunkurin da su ke yi na dinke barakar APC.

Alhaji Mai Mala Buni ya ce yawon da su ke yi domin sulhu a jam’iyyar APC ya fara kawo masu nasara a halin yanzu.

A cikin kwanakin nan, kwamitin rikon kwarya na Mai Mala Buni ya ziyarci jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da tsohon shugaban jam’iyya, Bisi Akande.

Da ake bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben APC a jihar Edo, Mai Mala Buni, ya ce ziyarar da su ka kai wa wadanda su ka kafa jam’iyyar APC ya fara kai ga ci.

KU KARANTA: APC ba ta ci zabe ba, mu mu ka yi murdiya a zaben 2016 – SSG

Mala Buni: An fara cin ma nasara bayan mun gana da Tinubu da Akande
Mai Mala Buni da su Bola Tinubu
Asali: Twitter

Sababbin shugabannin rikon-kwaryar APC sun gana da Bisi Akande da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gidajensu da ke jihar Osun da Legas.

Buni ya ke cewa tsarin da su ka kawo na zama da manyan jagororin jam’iyya domin a shawo kan rigimar cikin gidan da ta bijirowa jam'iyyar APC mai mulki.

A dalilin sabanin da aka samu a jam’iyyar APC ne majalisar koli ta NEC ta sauke duka shugabannin jam’iyyar APC na kasa.

Gwamnan na Yobe bai yi bayani dalla-dalla a kan abin da wannan tattaunawa ta su ta kunsa ba, amma da alamu cewa ana daf da samun nasara.

Ku na da labari cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shi ne aka nada a matsayin shugaban yakin neman zaben APC a zaben gwamnan jihar Edo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel