Kaduna ta samu miliyan N1.9 daga hannun wadanda suka karya dokar kulle cikin kwanaki 2

Kaduna ta samu miliyan N1.9 daga hannun wadanda suka karya dokar kulle cikin kwanaki 2

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta tara kudi har naira miliyan 1.9 cikin kwanaki biyu, daga wajen masu karya dokar kulle da aka sanya a jihar domin hana yaduwar cutar COVID-19.

Gwamnatin jihar ta ma’aikatar shari’a ta ce masu laifi 605 aka hukunta a tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a na makon da ya gabata, kan karya dokar kulle.

Ta kara da cewa “an samu kimanin N1,909,600 a matsayin tarar da aka ci masu laifin sannan aka baiwa wasu mutum 41 aikin gyara gari.”

Kaduna ta samu miliyan N1.9 daga hannun wadanda suka karya dokar kulle cikin kwanaki 2
Kaduna ta samu miliyan N1.9 daga hannun wadanda suka karya dokar kulle cikin kwanaki 2 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinar shari’a kuma Atoni Janar ta jihar, Aisha Dikko, ta ce an hukunta mutanen ne kan laifuffukan da suka hada da rashin sanya takunkumin hanci a cikin jama’a da kuma karya dokar hana zirga-zirga.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta kafa kotun-tafi-da-gidanka a ranar 24 ga watan Afrilu domin hukunta wadanda suka saba dokar kulle a wasu wurare kamar su Kakuri, Kawo, Magajin Gari, Rigasa, Sabon Tasha da Maraban Rido.

Sauran wuraren sun hada da Rigachukwu, iyakar Kaduna-Kano da kuma hanyar babban titin Abuja-Kaduna.

Kwamishinar ta yi gargadin cewa masu karya dokar na iya rasa ababen hawansu sannan a mallakawa gwamnati su.

Ta kara da cewa “wadanda suka karya dokar zama a gida sannan basu sanya takunkumin hanci ba za su biya tarar N5,000 kowannen su. A daya bangaren rashin bayar da tazara a tsakani zai sa a ci tarar mutum N7,000.

KU KARANTA KUMA: Kowa ya raina gajere ya taka kunama: El-Rufai ya fadi sunan jagoran tafiyarsu ta ‘Kungiyar gajerun Najeriya’

“Tuka babura da adaidaita ba tare da izini ba a lokacin kullen, da kuma tuka motoci, manyan tireloli da bas zai jawo a ci tarar mutum N5,000, N10,000, N20,000, N30,000, N20,000,” cewar ta.

A gefe guda, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da rasuwar majinyata biyu sakamakon annobar Coronavirus, kwanaki takwas bayan sanar da mutuwar farko da jihar ta fuskanta sakamakon cutar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a halin yanzu jihar Kaduna ta rasa mutum uku sakamakon annobar Coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel