Mutanenmu ba su yarda cewa covid-19 gaskiya ba ce - Mataimakin gwamnan Borno

Mutanenmu ba su yarda cewa covid-19 gaskiya ba ce - Mataimakin gwamnan Borno

Mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Kadafur, ya bayyana cewa wasu daga cikin jama'ar jihar ba su yadda da wanzuwar cutar Coronavirus ba.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, Kadafur, wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar Borno, ya kwatanta annobar da Boko Haram.

Ya ce yadda take kutsawa cikin jama'a na daidai da yadda mayakan ta'addancin Boko Haram ke shiga sassan kasar nan.

Yace duk da yadda take sake shiga wurare, wasu jama'a suna take dokar nisantar juna ta yadda suke zuwa jana'iza da kuma sallar jam'i.

Mutanenmu ba su yarda cewa covid-19 gaskiya ba ce - Mataimakin gwamnan Borno

Mutanenmu ba su yarda cewa covid-19 gaskiya ba ce - Mataimakin gwamnan Borno
Source: Twitter

Ya kwatanta lamarin da abun takaici.

"A lokacin da Boko Haram ta fara, mutane da yawa suna tsammanin wasa ne, har sai da ta shafesu. Wannan annobar wata nau'i ce irin Boko Haram kuma har yau wasu basu yadda da wanzuwar ta ba," Kadafur ya sanar a wata takarda da ya fitar.

KU KARANTA KUMA: Bayanai sun fito a kan musabbabin mutuwar babban sarki a Zamfara

"Ina ci gaba da jaddada cewa akwai cutar. A matsayin kwamitin yaki da cutar, za mu ci gaba da wayarwa da jama'a kai," yace.

Mutum 75 ne da suka hada da ma'aikatan lafiya 16 suka kamu da cutar a jihar Borno. An samu rasuwar mutum 11 duk a jihar.

Mataimakin gwamnan ya ce kwamitin na aiki tukuru don dakile yaduwar muguwar cutar a jihar.

Ya yi kira ga jama'ar jihar da su fahimci hatsarin da ke tattare da cutar, don haka a kiyaye dokokin da masana kiwon lafiya suka bada.

A wani labarin, mun ji cewa cutar coronavirus ta kashe dan majalisar jihar Nasarawa, Adamu Sulaiman, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Sulaiman ne majinyaci na farko da ya rasu sakamakon annobar a jihar Nasarawa tun bayan da aka gano cutar ta shiga jihar.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da mutuwar dan majalisar a yayin da yake jawabi ga manema labarai a garin Lafia, babban birnin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel