Covid-19: Gwamnatin tarayya ta zabtare kasafin kudin majalisar dokokin tarayya da N25.6bn

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta zabtare kasafin kudin majalisar dokokin tarayya da N25.6bn

Wasu bayanai masu karfi da suka billo a ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta zabtare kasafin kudin majalisar dokokin tarayya na 2020 da naira biliyan 25.6.

Hakan ya zamo kaso 20 cikin dari na naira biliyan 128 da aka lamunce wa majalisar dokokin tarayyar a kasafin kudin wannan shekarar.

A tuna cewa kasafin kudin da aka amincewa gwamnatin tarayya na shekarar 2020 ya kasance naira triliyan 10.3.

Amma aka rage shi zuwa naira triliyan 8 saboda barkewar annobar coronavirus wacce ta shafi farashin man fetur a duniya.

Gwamnatin na siyar da kowace gangar danyen mai guda kan dala 57 amma a yanzu farashin na tsakanin dala 20 da 25 ne.

Covid-19: Gwamnatin tarayya ta zabtare kasafin kudin majalisar dokokin tarayya da N25.6bn
Covid-19: Gwamnatin tarayya ta zabtare kasafin kudin majalisar dokokin tarayya da N25.6bn
Asali: Depositphotos

A sakamakon wannan lamari, an fahimci cewa za a zabtare kasafin kudin bangaren zartarwa, shari’a da na dokoki da kaso 20 cikin dari.

Bulaliyar majalisa, Muhammad Tahir Monguno ya tabbatar da cewar za a zabtare kasafin kudin majalisar dokokin kasar da kaso 20, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa an dakatar da batun naira biliyan 37 da aka nema domin gyara ginin majalisar dokokin.

KU KARANTA KUMA: Yan Abuja sun koka kan yadda ake gudunsu a garuruwansu na asali saboda Corona

A wani labarin kuma mun ji cewa, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta janye rokon da Ma'aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren kasa ta yi na neman tallafin na'uarar taimakawa numfashi ta 'ventilator' daga wurin attajirin kasar Amurka, Elon Musk domin yi wa masu fama da cutar coronavirus magani a Najeriya.

Mai kamfanin SpaceX kuma babban injiniyan kamfanin, Musk, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamisa cewa kamfaninsa tana da raran na'urorin taimakawa numfashin da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na Amurka (FDA) suka amince da ingancinsu.

"Muna da rarar ventilators da FDA ta amince da ingancin su. Za mu aike da asibitoci a kasashen duniya da kamfanin Tesla ke harka da su. Abinda muke bukata kawai shine a yi amfani da su nan take a taimakawa masu jinya ba wai a ajiye su a dakin ajiya ba," kamar yadda ya rubuta a Twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel