Sanatocin Najeriya 109 sun bada gudunmuwan rabin albashinsu don yakar Coronavirus

Sanatocin Najeriya 109 sun bada gudunmuwan rabin albashinsu don yakar Coronavirus

Mambobin majalisar dattawan Najeriya sun yanke shawarar ba da gudunmuwar rabin albashinsu fari daga watan Maris domin yakar cutar Coronavirus da ta addabi Najeriya.

Mukaddashin kakakin majalisar, Godiya Akwashiki, ya sanar da hakan ne ranar Litinin a wnai jawabi.

Jawabin yace: "Bayan shawara kan yadda ake bada gudunmuwa wajen ganin karshen annobar Coronavirus a Najeriya, majalisar dattawa na sanar da cewa fari daga watan Maris, sanatoci za su rika bada gudunmuwar rabin albashinsu na wata domin yakar wannan cutar."

"Yan majalisar dattawa za su cigaba da bada rabin albashinsu na wata har sai an an ga bayan cutar Coronavirus a Najeriya."

"Majalisar dattawar ta jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa kan namijin kokarin kare kasa daga annobar."

Sanatocin Najeriya 109 sun bada gudunmuwan rabin albashinsu don yakar Coronavirus
Sanatocin Najeriya 109 sun bada gudunmuwan rabin albashinsu don yakar Coronavirus
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel