Yanzu-yanzu: Sanatan YPP daya tilo ya tsallake rijiya da baya, kotu ta tabbatar da shi

Yanzu-yanzu: Sanatan YPP daya tilo ya tsallake rijiya da baya, kotu ta tabbatar da shi

Sanatan jamiyyar Young Progressives Party daya tilo a majalisar dattawan tarayya, Sanata Ifeanyi Uba, mai wakiltar Anambara ta kudu ya tsallake rijiya da baya a kotun daukaka kara.

A ranar alhamis, 19 ga Maris, kotun daukaka karar ta tabbatar masa da kujerarsa bayan babbar kotun tarayya dake Abuja ta kwace masa.

Yanzu-yanzu: Sanatan YPP daya tili ya tsallake rijiya da baya, kotu ta tabbatar da shi

Ifeanyi
Source: UGC

KU KARANTA Babu wanda ya kaiwa Kwankwaso hari - Mai magana da yawun Abba Gida-gida

A baya mun kawo muku labari cewa Alkali ya tsige Sanata Ifeanyi Ubah daga kan kujerar da ya ke kai a Majalisar dattawan Najeriya.

Alkalin babban kotun tarayya da ke zama a Kubwa, ya ba Ifeanyi Ubah rashin gaskiya a shari’ar da ake yi game da zaben Sanatan.

Mai shari’a Bello Kawu, ya tabbatar da hukuncin da aka yi a bara na cewa a karbe nasarar da aka ba Sanatan na YPP a zaben 2019.

An samu Sanata Ifeanyi Ubah da laifin amfani da jabun takardar shaidar jarrabawa ta NECO wajen shiga takarar ‘Dan majalisa.

Ifeanyi Ubah ya daukaka kara ne a kotun, ya na neman ayi fatali da rashin gaskiyar da aka ba shi a wani kotu, amma bai yi nasara ba.

Amma Kwanaki goma bayan an tsige Sanata Ifeanyi Ubah daga majalisar tarayya bisa zargin satifiket din bogi, hukumar NECO ta fito ta yi magana.

Hukumar jarrabawar kasa watau NECO, ta tabbatar da cewa Sanatan ya rubuta jarrabawar kammala sakandare, kuma ya lashe jarrabawar.

Mai girma Sanata Ifeanyi Ubah ne ya fitar da wannan labari a Ranar Litinin, 27 ga Watan Junairu, 2020 a shafinsa na sada zumunta na Facebook.

‘Dan majalisar da aka sallama ya ce hukumar NECO ta tabbatar da cewa takardun shaidar jarrabawarsa da ya gabatarwa INEC ba na jabu bane.

A cewarsa, a wata wasika da NECO ta aikawa kungiyar HURIWA ta Marubutan Najeriya, an tabbatar da sahihancin sakamakon jarrabawar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel