Daga zuwa gida jana'izar mahaifinta, sai ita ma ajali yayi halinsa sanadiyyar kasheta da kawunta yayi

Daga zuwa gida jana'izar mahaifinta, sai ita ma ajali yayi halinsa sanadiyyar kasheta da kawunta yayi

- Wani mutum mai suna Ambrose Owiriwa ya shiga hannun jami'an tsaro bayan da aka kama shi da laifin kashe 'yar yayanshi

- Lamarin ya faru ne lokacin da 'yar hatsaniya ta auku tsakaninsu bayan da taje gida Kirsimeti

- Dama can kawun ya taba sukar kanwarshi da wuka, ya tsigewa mai rasuwar kunne, sai a wannan shekarar ya kashe Olayile har lahira

Wani mutum mai suna Ambrose Owiriwa ya shiga hannun jami'an tsaro bayan da aka zargeshi da kashe 'yar dan uwanshi sakamakon wata karamar hayaniya da ta wanzu a tsakaninsu.

Mamaciyar ta samu zubar jini ta ciki ne kafin likitoci su tabbatar da mutuwarta. Kawun nata ya buga mata murhu ne a fuskarta da hancin ta.

An gano cewa Olayile ta rasu ne bayan shekara daya da aurenta kuma yayin da mahaifinta ke kwance a ma'adanar gawawwaki ba tare da an birne shi ba.

An kara da zargin Ambrose da cizon daya daga cikin kunnuwan Olayile tare da sukar 'yar uwarshi kafin a kama shi bayan kisan Olayile.

Daga zuwa gida jana'izar mahaifinta, sai ita ma ajali yayi halinsa sanadiyyar kasheta da kawunta yayi
Daga zuwa gida jana'izar mahaifinta, sai ita ma ajali yayi halinsa sanadiyyar kasheta da kawunta yayi
Asali: Facebook

Jennifer Louis ta rubuta: "Abun bakin ciki ne yadda kawu ya kashe kyakyawar 'yar yayanshi Olayile Owiriwa a Oroworokwu ta jihar Ribas. Taje gidansu ne don bikin kirsimeti amma sai karamin sa'in'sa ya auku tsakaninta da kawunta wanda ya kasheta har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa, Kawun Olayile ya taba tsinke mata kunne a shekarar da ta gabata kafin aurenta. Muna fatan Ubangiji yayi miki rahama Olayile Owiriwa.

Kamar yadda Wechie Platform Livingstone suka rubuta: "Allah sarki, wasu kawunnan sukan gwada karfinsu ne a kan 'ya'yan yayyinsu. Wannan nuna mulkin mallaka ne. Ka tsige mata kunne, ka taba sukar 'yar uwarka yanzu kuma ka halaka 'yar yayanka bayan da yake kwance a ma'adanar gawawwaki ko birneshi ba a yi ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel