Babu gaira babu dalili aboki ya daddatsa abokinshi da adda, jim kadan da kammala cin abincin su

Babu gaira babu dalili aboki ya daddatsa abokinshi da adda, jim kadan da kammala cin abincin su

- A yankin Oke-Oyi ne wani aboki ya daddatsa abokinshi da adda ba tare da dalili ba

- An gano cewa, Ibrahim Ajayi Allah tsohon ma'aikacin NNPC ne wanda yayi murabus kuma ya koma Oke-Oyi a jihar Kwara

- Tare suka ci abincin rana da wanda ake zargi da kisan Ajayi, an kuma kamashi da waya tare da adda mai jini a jiki

Mamaki da tsananin alhini ya shiga zukatan mutane bayan da abokin wani ma'aikacin matatar man fetur ta kasa ta NNPC ya kasheshi.

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, Ibrahim Ajayi Allah, yayi murabus daga aiki a NNPC kuma ya tashi daga Ogidi dake jihar Kogi zuwa Oke-Oyi dake kusa da Kwara. Bai da masaniyar cewa ba zai ga karshen shekarar ba. Barin aikinshi yasa ya sauya wajen zama amma abun haushin shine yadda aka kasheshi a ranar Juma'a.

Kamar yadda abokin mamacin ya sanar, Ajayi ya siya wani katon fili a Oke-Oyi inda ya hada alaka mai karfi da wanda ake zargin ya kasheshi.

"Yana yawo ko ina da mutumin. A takaice dai a ranar da ya kasheshi, sun ci abincin rana tare. Da yammaci ne ya daddatsa shi da takobi wajen karfe 5 na yamma," abokin Ajayi yace.

KU KARANTA: Zina yake da kanwata shine ma abinda yasa ya gyara musu gidansu - Budurwa ta tonawa Fasto asiri

"A lokacin da 'yan sanda suka duba gidan mutumin, sun samu wayar abokina da wasu abubuwanshi. Ya sanar da cewa shi ya kasheshi."

A lokacin da matar mamacin tayi magana da The Cable, Modinat wacce ke zama a Abuja ta roki 'yan sanda dasu gano tushen matsalar kuma kada su bar ran mijinta ya tafi a haka. Tace kafin a kasheshi, suna magana da mijinta ta waya a kullum.

Jami'an 'yan sandan yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin. Sun ce zasu mikashi zuwa sashin laifuka na musamman. Tunda wanda ake zargin ya amsa laifinshi bayan da aka kamashi da wayar mamacin tare da adda mai dauke da jini.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel