Wata babbar kotu a jihar Kano ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin kisa

Wata babbar kotu a jihar Kano ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin kisa

- Wata babbar kotu a jihar Kano mai daraja ta takwas, ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin kisa

- Hakan ya biyo bayan kamasu dumu-dumu da aka yi da laifin hadin kai wajen sata da kisan kai

- Har ila yau, kotun ta saki Kabiru Gayawa bayan da ta gano babu hannunsa a cikin zargin da ake masa

Wata babbar kotu a jihar Kano mai lamba takwas, ta yankewa wasu mutane biyu hukuncin kisa. Kotun karkashin jagorancin Jastis Usman Abba ya zartar da hukuncin kisan ne akan mutane biyu.

Tun a shekarar dubu biyu da sha uku, gwamnatin jihar ta gurfanar da mutanen bisa zarginsu da hadin baki wajen sata da kuma kisan kai, lamarin da mutanen suka musanta.

Lauyoyin gwamnati sun gabatar da shaidu har shida, sai dai kotun ta yi watsi da shaida ta hudu da masu kare kansu suka gabatar.

DUBA WANNAN: Masu zanga - zanga sun rufe hanyara Kaduna zuwa Abuja a kan sakamakon zaben kananan hukumomi

Kamar yadda kotun ta sanar, Aliyu Abubakar da Sanin Fulani sun shiga hannu ne bayan da aka kamasu dumu-dumu da laifin sata da kisan kai. A don haka ne aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rayata.

An kuma karawa Sanin Fulani shekaru bakwai a gidan maza saboda kama shi da aka yi da kayan sata.

Hakazalika, kotun ta ce ba zata fadi ra'ayinta a kan wanda ake zargin na farko ba, wato Tasiu Abdullahi, kasancewar ya rasu ne gidan gyaran hali.

Amma daga bisani, kotun ta wanke Kabiru Gayawa yayin da ta bukaci a sakesa yayi tafiyarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel