Sarkin Minna ya kallubalanci al'ummar musulmi kan neman ilimin addinin musulunci

Sarkin Minna ya kallubalanci al'ummar musulmi kan neman ilimin addinin musulunci

Sarkin Minna, Alhaji Umar Faruq Bahago ya yi kira ga al'ummar musulmi da kada su bari a bar su a baya wurin neman ilimin addinin musulunci da yace shine mafita ga kallubalen tsaro da sauran matsalolin rayuwa da ake fama da su.

A jawabinsa wurin taron gasar karatun al-qurani na shekara-shekara karo na 34 a jihar da aka yi a Minna, ya bukaci al'umma su yi amfani da ilimi da koyarwar da ke cikin Kura'ani domin kawo cigaba a kasar.

Sarkin ya kara da cewa neman ilimin addini da na boko wajibi ne ga dukkan al'umma maza da mata.

Ya ce dalilin shirya gasar shi ne zakulo wadanda za su wakilci jihar a gasar karatun Kur'ani na kasa da za a gudanar a jihar Legas.

Jihar Neja ce ta zama zakara a gasar da aka gudanar a bara a jihar Nasarawa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

Ya yi bayyanin cewa, "Amfanin masabakar Al-Kur'ani ba zai taba misaltuwa ba. Na farko dai Ibadah ce kuma halartan taron da ake karatun Kurani shima yana da ladarsa.

"Babban dalilin shine samun karin mutanen da suka haddace Kurani ta hanyar janyo hankulan al'umma musammam matasa wurin karatu da fahimtar koyarwar Kur'ani tare da aiki da koyarwasa kamar yadda malaman mu suka koyar."

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar ya ce ana shirin yi wa tsarin koyar da darasin addinin musulunci garambawul a jihar don shigo da haddar Kur'ani a ciki.

A cewarsa, tsarin shine tabbatar da cewa dalibai sun haddace Kur'ani mai girma a lokacin da za su shiga sashin babban sakandare.

Ya kuma yabawa wadanda suka shirya musabakar musamman yadda suka karrama jihar ta hanyar zama zakaru a gasar da aka gudanar a bara a jihar Nasarawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel