Yanzu-yanzu: An samu Firai Ministan Isra'ila da almundaha

Yanzu-yanzu: An samu Firai Ministan Isra'ila da almundaha

Atoni janar na kasar Isra'ila, Avichai Menadelblit ya samu Firai Ministan kasar Banjamin Natanyahu da laifin cin hanci da rashawa tare da cin amana kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a ranar Alhamis.

Avichai Menadelblit ya bayar da sanawar ne a ranar Alhamis kan tuhumar da ake yi wa Mista Netanyahu da hannu cikin karbar cin hanci da cin amana da ta kai dalla miliyan 500 tsakanin 2012 zuwa 2017.

Sai dai Mista Netanyahu ya musanta tuhumar da ake masa inda ya ce bita-da-kulli ne 'yan jam'iyyar adawa ke masa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Shugaba Reuven Rivlin ya bai wa Netanyahu damar samar da gwamnatin hadin gwiwa, amma har yanzu hakan bai samu ba.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai wa Kwamishina hari, sun kashe direbansa

Wasu kafafen yaada labarai na Isra'ila sun ruwaito cewa Mista Netanyahu yana fatan samar da wata doka da za ta hana a kama shi da laifi.

Sai dai rashin samun isasun kuri'u domin kafa gwamnati bayan zaben da aka gudanar ranar 17 ga watan Satumba ya jefa shi tsaka mai wuya.

Duk da hakan yana iya neman Majalisar Isra'ila ta bashi wata kariya ta musamman amma hakan ba zai yiwu duba da cewa ba a kafa gwamnati ba.

Mista Netanyahu mai shekaru 70 ya kasance a matsayin Farai Ministan Isra'ila tun 2009. A baya ya rike mukamin a 1996 da 1999.

Duk da rikice-rikicen cikin gida da ya ke fuskanta, ya cigaba da samun goyon bayan Shugaba Donald Trump na Amurka musamman tunda shugabanin biyu na hadin gwiwa wurin yaki da tsatsauran ra'ayoyi a Gabas ta tsakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel