Tirkashi: Wani dan majalisar Najeriya ya ciri tuta, ya nada hadimai 36

Tirkashi: Wani dan majalisar Najeriya ya ciri tuta, ya nada hadimai 36

- Dan majalisar tarayya mai wakiltar Balanga/Billiri a majalisar dattawa ya zabi hadimai 36

- Ya bayyana cewa, yayi hakan ne don samar musu da abinda zasu sa a bakin salatinsu

- Dan majalisar ya bayyana cewa, a cikin alawus dinsa zai dinga biyan kashi 80 na cikin hadiman inda Majalisar Dattawa za ta biya sauran kashi 20

A wani abu da ya kira 'Ba zan ci ni kadai ba,' Victor Mela Danzaria, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Balanga/Billiri a Majalisar Dattawa, ya nada hadimai 36.

Dan majalisar, a wata takardar da ya mika ga manema labarai a jiya a Gombe, yace, ya zabi hadiman ne don taimaka musu don samun abinda zasu sa a bakin salati.

Danzaria ya ce, duk mutanen da ya zaba sun goya mishi baya kuma sunyi aiki tukuru don ganin nasararsa ta tabbata. Ya kara da cewa, an yi takatsan-tsan wajen zabensu don tabbatar da duk mutanen mazabarsa sun samu wakilci.

DUBA WANNAN: Hukuncin kotun koli: Wanne mataki Atiku zai dauka nan gaba?

"Abin alfahari ne kuma wanda ba a taba yi ba, a ce an ba mutane 36 hanyar samun abinci. Zan biya kashi 80 daga cikinsu da alawus dina inda majalisar dattaws zata biya kadan daga cikinsu,"

"Na sanyawa hikimar nan sunan 'Ba zan ci ni kadai ba' don bawa mutanen da suka yi kokari wajen ganin nasarata damar samun na kansu," in ji shi.

Kamar yadda rahoton ya nuna, mutum daya ne babban mai bada shawara na musamman, uku mataimakan mai bada shawara na musamman, tara daga ciki mataimaka na matakin farko da kuma 23 daga ciki mataimaka na mataki na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel