Sarkin Dutse ya yabawa gwamnatin Najeriya bisa rufe kan iyaka da ta yi
Sarkin Dutse ta jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Nuhu Sanusi ya jinjinawa gwamnatin Najeriya bisa rufe kan iyakar kasar da ta yi.
Sarkin ya furta wannan kalamin ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar Miyetti Allah reshen Fanisau a fadarsa ranar Alhamis 25 ga watan Satumba. Inda ya ce rufe kan iyakar zai bamu damar sayen shinkafar da ake nomawa a nan gida.
KU KARANTA:Aikin ‘yan sanda:PSC ta dakatar da shirin karin mukamai da kuma daukar kuratan ‘yan sanda 10,000
Haka kuma ya kara da cewa, rufe kan iyakar zai taimakawa Najeriya wurin karin samun kudaden shiga. “Manoman shinkafan za su samu kwarin gwiwar noma shinkafa mai yawan gaske domin ciyar da gida da kuma kasashen waje.” Inji Sarkin.
Bugu da kari, Sarkin ya yi karin haske game da wasu kayan abinci da ake shigowa da su kasar nan musamman shinkafa, inda ya ce ana iya ajiyeta a dakin ajiyar hatsi har tsawon shekara goma kafin a shigo mana da ita kasarmu.
A wani labari mai kama da wannan zaku ji cewa, hukumar da ke sanya ido a kan lamuran ‘yan sanda wato PSC ta dakatar da daukar sabbin kurata 10,000 da rundunar ‘yan sandan Najeriya ke shirin yi.
Wannan kuwa ya biyo bayan rashin jituwa dake tsakanin hukumar da kuma Sufeto janar Mohammed Adamu wanda yake ganin a matsayinsa na shugaban ‘yan sanda zai iya cigaba da tantance daukar sabbin ma’aikatan.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng