Katsina: Yan bindiga sun gabatar da babban bukata da suke so a cika masu kafin su ajiye makamansu

Katsina: Yan bindiga sun gabatar da babban bukata da suke so a cika masu kafin su ajiye makamansu

Yan bindiga da ke fashi a Katsina a jiya Laraba, 4 ga watan Satumba, sun bayar da ka’idojin ajiye makamansu.

Sun bukaci a saki mambobinsu da ke tsare a gida yari daban-daban sannan sun nemi a duba yadda jami’an tsaro, sarakunan gargaji da alkalai ke karbe masu dabbobinsu.

Da yake magana a lokacin tattaunawa tsakaninsu da Gwamna Aminu Masari a kauyen Dankolo, sun bayyana cewa mafi akasarinsu sun shiga harkar fashi ne saboda kiyayyar da mutanen garin, jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da kuma alkalai ke nuna masu.

Idris Yayande, daya daga cikin yan bindigan yace: “Muna da korafi muma, mafi akasarin wasu daga cikin mutanenmu da aka kama kamar Alhaji Baldu, Alhaji Lawal da Ibrahim Nakutama wadanda aka kama bayan sun dawo daga hajji. Nima an kama ni kuma har yanzu, ba a fada mun laifin da na aikata ba. An tsare ni tsawon watanni 15 kafin aka sake ni.

“Tsawon watanni biyar da suka gabata, tun lokacin azumi da muka gana da al’umman, bamu kai hari akan su ba. Babu wani da muka yi garkuwa dashi, idan ka ji cewa wani abu mai kama da haka ya faru toh ba daga wannan sansanin bane. Babu shakka, akwai wurare da ake hare-hare da garkuwa da mutane saboda bamu da iko akan wadannan wurare, amma a wannan wuri da muka dauki rantsuwar dainawa, suna cikin kariya, muna iya bakin kokarinmu.

“Kuna ganin gonaki a yanzu wanda a baya uka sha alwashin cewa babu mai noma a cikinsu, amma a yanzu kuna ganin mutane na noma a ciki.”

Shugaban yan banga a yankin, Lawal Tsoho, ya shawarci gwanan da ya hankalta da wasu yan siyasa da manyan gwamnati da basa son wannan shiri na zaman lafiya ya cimma nasara.

KU KARANTA KUMA: Neman iko kan daukar aikin 'Yan Sanda ya kawo rigima tsakanin NPF da PSC

Da yake marani, Gwamna Masari ya tabbatar da cewar wasu yan bindiga na tsare sama da shekara 10, inda yace: “babu ta yadda za ku dunga ajiye mutane tsawon sama da shekara biyu ba tare da wani tuhuma. Don haka ga mutanen da za a saki akan beli, idan har yan sanda za su iya samun tuhuma a kansu, za mu duba lamarin.

“Burinmu shine kawo zaman lafiya a Katsina da arewa maso yamma, muna ganin mun fara dauko hanya da kyau kuma babu abunda yafi zaman lafiya da sulhu. Da zaran kun fara tattaunawa, babu shakka za a samu mafita.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel