Kasar Saudiya za ta fara barin mata suyi tafiya ba tare da muharramansu ba – Rahoto

Kasar Saudiya za ta fara barin mata suyi tafiya ba tare da muharramansu ba – Rahoto

-Kasar Saudiya ta fito da sabuwar dokar barin mata suyi tafiya ba tare da muharramansu ba

-Jaridar Okaz ta kasar Saudiyan ce ta fitar da wannan labarin a ranar Alhamis inda take cewa Sarki Salman Bin Abdulaziz ya amince da wannan doka

-Ana sa ran wannan dokar za ta fara aiki ne a karshen watan Agusta kamar yadda ofishin jakadancin Saudiya dake Amurka ya fadi

Kasar Saudiya za ta fara barin mata suyi tafiya zuwa kasashen waje ba tare da izini ko kuma rakiyar muharramansu ba. Wannan abu zai kawo karshen wani takunkumi da mata ke fama da shi a kasar wanda ya dade yana shan suka daga kasashen duniya daban-daban.

Hukumomin kasar ta Saudiya sunyi kwaskwarima wa dokar mallakar takardun fita kasar waje, ta yadda duk macen da ta haura shekaru 21 za ta iya mallakar fasfo tare kuma da barin kasar ba tare da muharraminta ba.

KU KARANTA:Gwamnatin tarayya ta tsamo ‘yan Najeriya miliyan 5 daga matsanancin talauci a shekara 3 – Buhari

Jaridar Okaz wadda ke wallafa labaranta cikin harshen turanci a kasar ta Saudiya ce ta fitar da wanna rahoton ranar Alhamis, inda take cewa, wannan sabuwar dokar ta samu amincewar Sarki Salman Bin Abdulaziz.

Fadar masarautar ta Saudiya ta wallafa wani bayani a shafinta na tuwita inda take cewa, kwaskwarimar da aka yiwa dokar tafiya kasar waje da kuma ta yin aikin gwamnati ga mata zasu kasance cikin sabon mujalladin kundin tsarin dokokin kasar.

Har ila yau, ofishin jakadancin Saudiya dake Washington a kasar Amurka ya ce, wannan sabuwar dokar za ta fara aiki ne a karshen watan Agusta. “ A karkashin wannan dokar mata na da ikon neman fasfo da kansu kamar yadda maza ke zuwa su nema.” A cewar ofishin jakadancin.

Idan baku manta ba a kwanakin baya, masarautar kasar Saudiya ta sauya wasu dokokin kasar inda a ciki hadda barin mata su tuka mota da kansu wanda a da can ba suyi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel