Manoma daga kasar Koriya sun iso Najeriya don hadin gwiwa kan noman shinkafa

Manoma daga kasar Koriya sun iso Najeriya don hadin gwiwa kan noman shinkafa

Wata tawagar mutane takwas na masu zuba jari daga kasar Koriya ta Kudu, sun ziyarci jihar Kaduna tare da kudirin zuba jari a harkar noman shinkafa.

Mutanen yan kasar Koriya ta Kudu, wadanda suka kware a fannin noman shinkafa, sun yi shirin hada hannu da jihar ta hanyar hada kai da gidauniyar kamfanin Dangote.

Kungiyar Dangote ta dade tana zuba hannun jari a harkar noman shinkafa a jihar ta hanyar shiri dake kawo hadin kai.

Yan Koriya masu zuba jari a noman shinkafa za su hada gwiwa da Jigawa
Yan Koriya masu zuba jari a noman shinkafa za su hada gwiwa da Jigawa
Asali: Depositphotos

Yayinda suke magana, jagoran kungiyar yan Koriyan, Kim Byeong Sa, ya bayyana a lokacin da kungiyar ta kai ziyara ga gwamna, Muhammad Badaru Abubakar cewa sun ziyarci jihar ne don fara tattaunawa tare da gwamnatin jihar kan shirin bunkasa noman shinkafa a jihar.

Sam wanda ya kasance babban daraktan kungiyar Gyeongsangbukdo, ya ce suna aiki kut-da-kut da kungiyar Dangote, wanda ya kasance da kasuwanci a jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: PDP ta kauracewa taron gabatar da takardun shaidar cin zabe a Kano

A nashi bangaren, Gwamna Badaru, yace akalla kashi 70 na al’umman jihar manoma ne, inda ya kara da cewa tare da wannan dangantakar, jihar na a tafarkin samun nasara matuka a fannin noman shinkafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel