Yadda zan yi mulkin jihar Bauchi – Bala Mohammed

Yadda zan yi mulkin jihar Bauchi – Bala Mohammed

Zababben gwamnan jihar Bauchi wanda yayi takara a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bala Mohammed, ya bayyana cewa babban abunda zai sanya a gaba a yanzu shne inganta rayuwar al’umman jihar Bauchi.

Ya jinjina wa kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara akan namjin kokari da tarin goyon bayan da ya nuna masa a wannan gwagwarmaya da aka yi.

“Ina mai godiya a gare ku al’umman jihar Bauchi akan irin wannan hallaci da kuka nuna min. Ina mai tabbatar muku cewa ba zan baku kunya ba. Zan rike kowa a matsayin daya sannan zan yi muku aiki domin dawo da martabar jihar Bauchi.

Yadda zan yi mulkin jihar Bauchi – Bala Mohammed
Yadda zan yi mulkin jihar Bauchi – Bala Mohammed
Asali: Twitter

“Wajibi ne in jinjina wa kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da wadanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin Allah ya bamu nasara a wannan tafiya."

Sanata Bala ya kara da cewa gwamnatin sa za ta maida hankali ne wajen bunkasa ayyukan noma da kasuwanci. Sannan da inganta Ilimi da samar da ayyukan yi a fadin jihar.

KU KARANTA KUMA: Jihar Bauchi ba za ta sake goya wa azzalumi baya ba — Dogara

“Wani abu da faranta min rai shine ganin irin mataimakin da na dauka, wato sanata Baba Tela haziki ne kuma ya wakilci jama a majalisar dattawa. Hakan zai bamu daman tsara ayyukan ci gaba ga mutanen jihar Bauchi."

Da yake bayyana sakamakon zaben Malamin zabe na jihar Bauchi Mohammed Kyari ya ce Sanata Bala ya samu kuri’u 515,113, sannan gwamna mai ci Muhammed Abubakar ya samu kuri’u 500, 625.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel