Manyan Sojojin sama na Najeriya sun yi wani taro domin inganta tsaro

Manyan Sojojin sama na Najeriya sun yi wani taro domin inganta tsaro

Dakarun Sojojin sama na Najeriya sun soma wani taro da aka shirya domin gyara sha’anin tsaro. Kamar yadda mu ka samu labari, an fara wannan babban taro ne a Ranar Talata 19 ga Watan Maris.

Manyan Sojojin sama na Najeriya sun yi wani taro domin inganta tsaro
Manyan Sojojin sama a wajen wani taro jiya a Abuja
Asali: Twitter

Rundunar sojin saman na kasar su na wannan zama ne a dakin taro na Air Marshal Umar Blue Room da ke Hedikwatar su a babban birnin tarayya Abuja. Wannan ne karon farko da aka shirya wannan taro a gidan Sojin kasar.

Taken wannan zama shi ne “Enhancing Force Protection of NAF Bases for Effective Force Projection”. A ranar farko da aka fara wannan taro, an gabatar da takardu 2. Yau ne kuma ake sa rai za a sake gabatar da wata takardar.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun far ma wasu masallata a hanyar zuwa masallaci a Osun

Shugaban hafsun sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya samu tofawa taron albarka ta hanyar aika wani babban jami’i mai suna Air Vice Marshal Emmanuel Anebi ya wakilce sa a zaman da ake yi na kwana 2.

Air Marshal Sadique Abubakar a jawabin da aka gabatar a madadin sa, ya bayyana irin gyare-gyaren da aka yi a gidan sojin sama na kasar domin kawo karshen irin rikicin da ake fama da su a wasu bangarori na fadin Najeriya.

KU KARANTA: An soma yin nisa a kan batun hako danyen fetur a Arewa - NNPC

Shugaban sojin saman kasar yayi kira ga Dakarun da su ka halarci wannan zama da su yi aiki da abin da su ka koya a aikace. Haka zalika Sadique Abubakar ya yabawa kokarin da jami’an sa su kayi a zaben Najeriya da aka yi.

Shugaban gidan horaswa na gidan sojin saman na Najeriya, AVM Oladayo Amao, yace wannan gawurtaccen taro da aka shirya ya nuna irin kokarin CAS Sadique Abubakar. Ibikunle Daramola ya rahoto wannan labari a jiya.

Sojojin sun yi wani taron musamman jiya inda Air Vice Marshal Emmanuel Anebi ya wakilce CAS a zaman da ake yi. Ibikunle Daramola wanda ke magana a madadin sojojin saman kasar ya bayyana wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel