Kisan musulmai: 'Yan sandan Ostireliya sun bincike gidaje 2 da ke da alaka da dan bindiga

Kisan musulmai: 'Yan sandan Ostireliya sun bincike gidaje 2 da ke da alaka da dan bindiga

Yan sandan kasar Ostireliya sun sun yi wa wasu gidaje biyu kawanya sannan kuma suka yi masu binciken kwa-kwaf dake da alaka da dan bindigar nan da ya shiga masallaci a Nuyuzilan ya kashe musulmai akalla 50 a satin da ya gabata.

Gidajen dai kamar yadda muka samu, yan sandan kasar ta Ostireliya sun bincike su ne ranar Litinin kuma gidajen suna a wasu manyan garurun dake kudacin kasa inda kuma aka ce a nan ne dan ta'adan ya tashi.

Kisan musulmai: 'Yan sandan Ostireliya sun bincike gidaje 2 da ke da alaka da dan bindiga
Kisan musulmai: 'Yan sandan Ostireliya sun bincike gidaje 2 da ke da alaka da dan bindiga
Asali: UGC

KU KARANTA: INEC ta fitar da sabbin bayanai game da zaben Adamawa

Legit.ng ta samu haka zalika cewa yan sandan sun bayyana jin dadin su akan yadda suka ce 'yan uwan dan ta'addan suna basu hadin kai sosai wajen binciken da suke yi akan dan uwan nasu.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa mun labarta maku cewa Babban wanda ake tuhuma da laifin aikata ta'asar ta'addancin kisan musulmai masu sallah har mutum 49 a kasar Nuyuzilan ranar Juma'ar da ta gabata mai suna Brenton Tarrant ya gurfana a gaban wata kotun kasar domin fara shari'ar sa.

Kamar dai yadda muka samu, Brenton Tarrant wanda ke zaman dan asalin kasar Ostireliya mai shekaru 28 a duniya ya bayyana ne a akurkin wadanda ake tuhuma sanye da kayan fursuna kuma hannayen sa daure da ankwa domin soma shari'ar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel