Sharhi: Muhimman bayanai game da Mai Mala Buni, sabon gwamnan Yobe

Sharhi: Muhimman bayanai game da Mai Mala Buni, sabon gwamnan Yobe

Da yawa sun sha fadin cewa, zai zama abun mamaki, kusan kamar lamarin da ba zai iya faruwa ba, ace wai har a samu wani dan takarar gwamnan a jihar Yobe da zai iya karawa da babbar kusar jam'iyya mai mulki ta APC, ba ma wai batun kayar da dan takarar jam'iyyar ba, Mai Mala Buni, a zaben gwamnan jihar da aka gudanar.

Duba da nasabarsa ta bangaren siyasa kasancewarsa mai jama'a a fadin kasar, Mai Mala Buni zai kasance babban jari ga jihar Yobe saboda himmarsa ta kai jihar a tudun mun-tsira a fagen samo romon demokaradiyya daga gwamnatin tarayya.

Bayan kammala zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a ranar Asabar 9 ga watan Maris, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Mai Mala Buni a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Yobe, karkashin jam'iyyar APC da kuri'u 444,013, inda ya bashi damar lallasa Umar Iliya Damagun na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 95,703.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: An nemi Onnoghen a kotun CCT an rasa saboda ciwon hakori

Sharhi: Muhimman bayanai game da Mai Mala Buni, sabon gwamnan Yobe:

1. Mai Mala Buni ya fara siyasarsa ne a matsayin kansila inda daga bisani ya zama shugaban jam'iyyar ACD na farko a jihar, jam'iyyar da ta tsaya takarar zaben 2007 a matsayin jam'iyyar AC.

2. Daga bisani Mai Mala Buni ya zama mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Yobe akan harkokin jam'iyyu na cikin jihar inda daga bisani aka kara masa matsayi zuwa mukamin mashawarci na musamman ga gwamnan kan harkokin siyasa da majalisar dokokin jihar.

3. Daga nan ne aka nada Mai Mala Buni a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar ANPP na jihar kuma sakataren jam'iyyar APC na kasa a lokacin da aka kafata.

4. Mai Mala Buni yana da matakin karatu na Diploma da Degree.

Kamar yadda kowa ya sani, jihar Yobe ta kasance jihar da ke fuskantar matsaloli da dama, da suka hada da rikicin 'yan ta'adda da kuma durkushewar tattalin arziki. Kasancewar gwamnan jihar mai barin gado, Mr Gaidam ya yi hobbasa wajen gina jihar da kuma baiwa al'ummar jihar kwarin guiwa na kyakkyawar makoma a nan gaba, a yanzu haka dai idanuwa sun koma kan Mai Mala Buni, na ganin ya dora daga irin ayyukan da gwamna Gaidam ya ke yi na ganin jihar ta ci gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel