Kazamar siyasa: 'Yan daba dauke da muggan makamai sun kai wa kwamishin Tambuwal hari
Wasu 'yan bangar siyasa wadanda ake zargin magoya bayan jam’iyyar APC ne sun kai farmaki a gidan Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Sakkwato Barista Sulaiman Usman (SAN) a yammacin jiya tare da muzgunawa jama’a.
Da yake yi wa nanema labarai bayani a Cibiyar Lauyoyi ta Gamzaki a Arkilla, Babban Lauyan Nijeriya, Barista Sulaiman Usman ya bayyana cewar a lokacin da lamarin ya faru yana wajen yakin neman zaben PDP a Karamar hukumar Kware.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Zaben gwamnoni a jahohi 4 da za'a sha gumurzu
A cewar sa 'yan bangar siyasar sun yi aika-aikar ne da hadin bakin wasu jami'an 'yan sandan jihar da kuma wani dan dabar da ake cewa Bashiru Marar-Guiwa.
Kwamishinan ya bayyana cewar wannan ba shine karo na farko ba da hakan ke faruwa domin kuwa hakan ta faru a baya a shekarar 2008 a filin jirgi zai je Abuja daga Sakkwato shekaru 10 da suka gabata.
Daga karshe dai, kwamishinan yayi kira ga Kwamishinan ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar da su dauki matakin da ya kamata ta hanyar zakulo wadanda lamarin ya shafa tare da hukunta su domin ya zama darasi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng