Da dumin sa: Atiku Abubakar ya aike da muhimmin sako zuwa ga masoyan sa kafin zaben gwamna
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar ya aike da sakon bidiyo zuwa ga masoyan sa kan zaben gwamnonin ranar Asabar.
Atiku a ranar Alhamis din nan ce dai ya aike da sakon faifan bidiyon ne ta hanyar dora shi a shafin sa na dandalin sadarwar zamanin Tuwita yana mai kiran su su fita su kadawa jam'iyyar sa ta PDP da dukkan 'yan takarar ta a dukkan matakai.

Asali: UGC
KU KARANTA: Jahohin Arewa 4 da za'a tafka gumurzu a zaben Gwamna
Legit.ng Hausa ta samu cewa Atiku Abubakar ya yi anfani da wannan damar kuma ya godewa 'yan kasar musamman 'yan jam'iyyar PDP da suka fito kwan su da kwarkwata suka zabi jam'iyyar su da shi kan shi a zaben da aka gudanar sati biyu da suka shude.
Ga dai bidiyon nan:
A wani labarin kuma, Sashin dake kula da manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Yaba, jihar Legas ya fara gudanar da bincike bisa zargin cin hanci da ake yiwa DPO mai kula da sashin Pen Cinema mai suma Harrison Nwabuisi.
Majiyarmu ta bayyana mana cewa, DPO tare da wandasu jami’an ‘yan sanda ana zargin sune da amsar na goro daga wajen mazauna unguwar Alimi Ogunyemi dake Ijeiye.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng