Zaben 2019: Jerin malaman addini 5 da suka kunyata tare da Atiku Abubakar

Zaben 2019: Jerin malaman addini 5 da suka kunyata tare da Atiku Abubakar

Yayin da ake ta kara tattara bayanan abubuwan da suka faru gabanin gudanar da zabukan shugaban kasa a tarayyar Najeriya da ma lokacin zabukan, mun tattaro maku wasu muhimman batutuwa ma da ya kamata mu yi nazarin su yanzu.

Najeriya dai kasa ce da addini da kuma malamai ke da matukar tasiri da kuma muhimmaci a rayuwar 'yan kasar. Wannan kuma ya hada a tsakanin dukkan mabiya manyan addinan guda biyu watau musulunci da kuma kiristanci.

Zaben 2019: Jerin malaman addini 5 da suka kunyata tare da Atiku Abubakar
Zaben 2019: Jerin malaman addini 5 da suka kunyata tare da Atiku Abubakar
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan Rahama Sadau tana talla sun dauki hankali

Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa a wannan zaben da ya gudana malamai sun taka muhimmiyar rawa inda kuma ake tunanin a lokuta da dama kalaman su sun yi matukar tasiri a zukatan masu zabe.

A gabanin zaben dai mun samu cewa malamai da dama musamman ma na addinin kirista sun yi ta ikirarin karbar wahayi cewar dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ne zai lashe zaben.

Sai dai kuma an yi zaben kuma akasin hakan ne ta tabbata domin kuwa shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben a karo na biyu da tazarar kuri'u sama da miliyan hudu.

Ga dai jerin sunayen wasu malaman da suka yi hasashen lashe zaben Atiku Abubakar din kuma suka ji kunya:

1. Wani ne mai da'awar annabta mai suna Udoka Daniel Okechukwu a watan Disembar bara.

2. Shima dai yana da'awar annabta. Sunan sa Isa El-Buba.

3. Fasto Wale Olagunju

4. Fasto Samuel Akinbodunse

5. Fasto Primate. E.O. Akeju

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel