Da dumin sa: EFCC ta damke mai damfarar mutane da sunan Hamid Ali

Da dumin sa: EFCC ta damke mai damfarar mutane da sunan Hamid Ali

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta sanar da samun nasarar cafke wani mai suna Azeez Afolayan da ya ke damfarar mutane da sunan Hamid Ali.

Kamar yadda muka samu dai, shi Azeez Afolayan wanda yanzu haka yake garkame a dakunan ajiyar masu laifi na hukumar ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), ya shahara ne wajen karbar kudaden mutane da sunan zai samar masu aiki a hukumar Kwastam.

Da dumin sa: EFCC ta damke mai damfarar mutane da sunan Hamid Ali
Da dumin sa: EFCC ta damke mai damfarar mutane da sunan Hamid Ali
Asali: Facebook

KU KARANTA: An kama 'yan luwadi 3 a jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta samu cewa hukumar ta EFCC ta soma haka ma shi Mista Azeez din tarko ne biyo bayan korafi da suka samu daga wurin mutane da dama na cewa yana damfarar jama'a.

Tuni dai har an kama shi kuma kamar yadda muka samu bai ba shari'a wahala ba don kuwa ya amsa laifin sa tare da bayyana cewa tun da ya fara sana'ar a shekarar 2017, mutum 5 kawai ya damfara.

Mista Tony Orilade dake zaman jami'in hulda da jama'a na hukumar ta EFCC a cikin sanarwar manema labarai da ya fitar ya bayyana cewa kawo yanzu dan damfarar ya damfari mutane akalla Naira miliyan 1.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel