Ba magudi bane, dalilan da suka sa Buhari ya tara kuri'u a arewa maso gabas - Ndume

Ba magudi bane, dalilan da suka sa Buhari ya tara kuri'u a arewa maso gabas - Ndume

- Kwanciyar lafiyar da aka samu a arewa maso gabas ya bada gudummawa wajen samun kuri'u da dama da aka kadawa Buhari

- Duk da cewa dage zaben da akayi ya kawo cikas wajen fitowar masu kada kuri'ar

- Wancan karon daya gabata mun bawa shugaban kasar kuri'u kusan rabin miliyan a wannan karon kuma mun bada sama da 800

Ba magudi bane, dalilan da suka sa Buhari ya tara kuri'u a arewa maso gabas - Ndume
Ba magudi bane, dalilan da suka sa Buhari ya tara kuri'u a arewa maso gabas - Ndume
Asali: UGC

Sanatan dake wakiltar arewa maso gabashin Borno Sen Ali Ndume yace kwanciyar hankalin da suka samu ya taimaka kwarai wajen yawan kuri'un da shugaban kasa Muhammad Buhari ya samu a zaben daya gabata a ranar Asabar.

Ndume ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Villa yayin da suke tattaunawa da ragowar abokan aikin sa bayan ziyarar da suka kaiwa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Duk da cewar yayi tunanin za'a samu kuri'u sama da haka a yankin nasa.

Daraktan kamfen shugaban kasa a jam'iyar APC yace dage zaben da akayi ya kawo nakasu a bangaren futuwar masu kada kuri'a a yankin.

"Bari na fara da cewa a shekara ta 2015 shugaban kasar ya samu kuri'u kusan rabin miliyan yayin da kuma a wannan zaben ya samu sama da 800 a jihar ta Borno wanda hakan ya bashi damar samun kaso 95% kuma hakan ya samu ne sanadiyyar kwanciyar hankali da aka samu a Borno sama da shekara ta 2015."

GA WANNAN: Matakan da Atiku ke dauka ya zuwa yanzu, bayan ya sha kaye a hannun shugaban kasa Buhari

"Naso mu bashi kaso 97% amma duk da hakan ma an samu cigaba sama da baya."

Ndume ya kara da cewa zasuyi kokari a zaben gwamnoni da zai gudana wajen ganin jam'iyar APC ce ta lashe zaben ta hanyar kada kuri'un su.

A halin yanzu jam'iyar APC tana da sanatoci 64 kuma tana addu'ar samun kari akan hakan,jam'iyar bata fatan maimaita kuskuren da tayi a baya akan sanatocin.

Yace "Idan ka aikata kuskure kana amfani da wannan kuskuren ne wajen yin gyara a gaba saboda haka ne Mike burin samar da nagartacciyar majalisar tarayya da yarda Allah".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel