Zaben Shugaban kasa: Abubuwa 4 da suka sa Buhari ya doke Atiku

Zaben Shugaban kasa: Abubuwa 4 da suka sa Buhari ya doke Atiku

Ana ci gaba da yamutsa gashin baki tsakanin yan Najeriya da wasu masu fada aji a kasar tun bayan da hukumar zabe na kasa (INEC) ta kaddamar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

Yayinda wasu ke murna akan haka wasu sun cika da alhini akan faduwar da dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar yayi bayan hakan ya zo masu a bazata.

A yanzu haka dai shugabannin PDP sun nuna rashin amincewa da sakamakon zaben da INEC ta fitar, inda suka ki sanya hannu akan takardar sakamakon.

Ga wasu dalilai biyar da suka sa shugaban kasar mai shekara 76, ya yi nasara kan Atiku Abubakar, wanda ya taimaka masa wurin samun nasara a 2015.

1. Rashin hadin kan jam'iyyar PDP

Ganin yadda jam'iyyar PDP ta sha kaye a zaben 2015 bayan shafe shekara 16 a kan kujerar mulki, an yi zaton cewa za ta kimtsa tare da hada kanta da yin nazari kan matsalolin da ta fuskanta.

Sai dai an samu sabanin haka, inda wasu manyan jam'iyyarda wadanda suka amfana da mulkinta suka ja baya, suka bar ragamar a hannun baki irinsu Ali Modou Sharif, abin da ya jefa ta cikin rudani.

Ba su farga ba sai dab da zaben na bana. Hakan kuma a cewar Dr Suleiman A Suleiman na Jami'ar Amurka da ke Yola (AUN), ya sa sun rasa wata takamaimiyar alkibla, kuma sun yi kamfe maras armashi.

2. Tasirin yankin da zai karbi shugabanci a 2023

Batun yankin da zai karbi ragamar shugabancin kasar a zabe na gaba idan Buhari ya kammala wa'adinsa na biyu na daga cikin abubuwan da suka taka rawa wurin samun nasararsa.

Tsarin zaben kasar dai ya dogara ne kan karba-karba tsakanin Kudu da Arewa.

3. Yan Arewa sun yi wa Buhari halacci

Irin kyakkyawar alaka da kaunar da take tsakanin shugaban kasa Buhari da magoya bayansa duk da kalubalen da gwamnatinsa ta fuskanta a shekara hudun da ya shafe a kan mulki na daga cikin abunda ya bashi nasara.

Masoyansa sun tsaya tsayin-daka a bayansa a zaben 2019 kamar yadda suka saba yi masa tun shekarar 2003.

Mafi yawan kuri'un da ya samu sun fiuto ne daga yankin Arewa maso Yamma da maso Gabas, inda kuma a nan ne Atiku Abubakar ya sha mummuna kaye, kuma anan ne ya rasa damarsa ta karshe ta zama shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Nasarar zabe: Yan Igbo sun taya Shugaban kasa Buhari murna

4. Karbuwar da shirin yaki da cin hanci da rashawa ya samu a wajen jama'a

Wani abu da ake ganin ya taka rawa wurin sake zaben Shugaba Buhari shi ne sakon ya nuna cewa na yaki da cin hanci da rashawa, wanda kuma yana tasiri a zukatan talakawa, duk da cewa wasu na ganin babu wata gagarumar nasara da ya cimma a fannin.

Jama'a na yi masa kallon mutumin da yake fafutuka domin su, kuma wanda za su iya amince wa kan amanarsu.

Ba ya ga arewacin Najeriya, sakon yana kuma tasiri a wasu sassan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel