Zaben 2019: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun zargi Obasanjo da ci-da-zuci

Zaben 2019: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun zargi Obasanjo da ci-da-zuci

- An yi kira ga daukacin 'yan Nigeria da su tashi tsaye domin yakar duk wani yunkuri da Obasanjo ya ke yi na ganin ya hana ci gaban kasar da dorewar tattalin arziki

- AriseNigeria, wata kungiyar 'yan Nigeria mazauna kasashen waje ta caccaki irin zuci-zucin Obasanjo na ganin cewa PDP ta dare mulkin kasar

- Ta kuma gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta tabbata ta gudanar da sahihin zabe a kasar

An yi kira ga daukacin 'yan Nigeria da su tashi tsaye domin yakar duk wani yunkuri da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ke yi na ganin ya hana ruwa gudu a bangaren ci gaban kasar da dorewar tattalin arziki.

Ku farka 'yan Nigeria (AriseNigeria), wata kungiyar 'yan Nigeria mazauna kasashen waje, wacce ta yi wannan kiran a ranar Litinin, ta yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasar na ci-da-zuci na ganin ya dora sabon shugaban kasa ta kowanne hali.

Kungiyar a cikin wata sanarwar bayan taro da ta fitar jim kadan bayan kammala wani taronta na gaggawa, domin duba yanayin tafiyar da harkokin Nigeria, ta caccaki irin dogon buri da zuci-zucin Obasanjo na ganin cewa PDP ta dare mulkin kasar.

KARANTA WANNAN: Ku daina alakanta ayyukanmu da Lawal Daura - SSS ta gargadi 'yan Nigeria

Zaben 2019: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun zargi Obasanjo da ci-da-zuci
Zaben 2019: Yan Nigeria mazauna kasashen waje sun zargi Obasanjo da ci-da-zuci
Asali: UGC

Takardar bayan taron na dauke da sa hannun shugabanta, Dr Philip Idaewor da kuma amincewar kodinetocinta na fadin duniyar, da suka hada da: Charles Eze, Prof. Adesugun Labinjo USA, Mr. Ayoola Lawal (Sweden), Chief Balogun (France), Mr. Chima Ibezim (Italy), Mr. Adeayo Tella (Spain), Mr. Bola Babarinde (South Africa), Mr. Hammeed Adefioye (Republic of Irleland), Mr. Marthins Sadoh (Holland), Mr Ogunwede Lombrado (Germany), Mr. Niyi Agbelese (Switzerland), Mr. Charles Michelleti (Ghana), Engr David Onmeje (Scotland), Mr. Eric Ayoola (UK), Mr. Ikem Chinedu (UK), Mr. David Abraham (South Korea)

Kungiyar ta ce Obasanjo a ci-da-zucinsa na son ganin ya rufe badakalar cin hanci da rashawarsa da kuma son gujewa bincike kan gazawar gwamnatinsa tsakanin 1999 da 2007, na iya bakin kokarinsa na ganin Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu nasara a zaben shugaban kasar da aka mayar zuwa ranar 23 ga watan Fabreru.

Ta kuma gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta tabbata ta gudanar da sahihin zabe a kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel