Zaben shugaban kasa: Kar mu kuskura mu bari Nigeria ta koma hannun maha'inta - Buhari

Zaben shugaban kasa: Kar mu kuskura mu bari Nigeria ta koma hannun maha'inta - Buhari

- Buhari ya roki jama'ar kasar da kar su kuskura su bari Nigeria ta koma hannun marasa kishi, wadanda za su kara durkusar da ita fiye da yadda suka yi a baya

- Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu nasara akan bangarori uku na tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa

- Buhari ya ce burin jam'iyyar adawa shine sayar da kadarorin da kasar ta mallaka tare da yin facaka da arzikin ma'adanan kasar

A gabanin zaben ranar 16 ga watan Fabreru, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya roki 'yan Nigeria da kar su kuskura su bari Nigeria ta koma hannun marara kishi, wadanda za su kara durkusar da ita fiye da yadda suka yi a shekarun baya.

Shugaban kasa Buhari wanda ya yi wannan rokon a lokacin kaddamar da wani littafi mai taken "Nigeria akan turba ta gaskiya, tunkarar dorewar zaman lafiya da ci gaba" a babban dakin taron na cikin fadar shugaban kasa, Abuja, ya ce gwamnatinsa ta cika dukkanin alkawuran da ta daukarwa 'yan Nigeria a lokacin yakin neman zaben 2015.

Ya ce: "La'akari da cewa za a fara gudanar da zabukan 2019 nan da mako daya, hakika wannan taro na yau na da matukar muhimmanci musamman yadda ya kara haska irin nasarorin da gwamnatin jam'iyyar APC ta samu tun hawanta mulki bayan zaben 2015."

KARANTA WANNAN: Fadan manya: Ni ma biloniya ne kafin na zama gwamna - Ortom ya caccaki Akume

Zaben shugaban kasa: Kar mu kuskura mu bari Nigeria ta koma hannun maha'inta - Buhari
Zaben shugaban kasa: Kar mu kuskura mu bari Nigeria ta koma hannun maha'inta - Buhari
Asali: Facebook

Buhari ya ce gwamnatinsa ta dauki tsarin CANJI wanda kuma ya haifar da d'a mai ido musamman akan bangarori uku na tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa, yana mai cewa abubuwa za su karu idan har 'yan Nigeria suka bashi damar kai kasar zuwa mataki na gaba.

"Daga kan farfado da tattalin arziki har zuwa dorewar muradun karni, kakkabe 'yan ta'addan Boko Haram, yaki da cin hanci da rashawa, hakika tarihi ba zai taba mantawa da wannan gwamnati a matsayin wacce ta cika alkawuran da ta dauka, kuma tarihi zai yi adalci a lokacin da muke kokarin kai kasar zuwa mataki na gaba.

"Duba da irin tarbar da muke samu a duk inda muka je kaddamar da yakin zabenmu a fadin kasar cikin 'yan makonnin nan, ina da yakinin cewa akwai bukatar ci gaba da kasancewa tare da jam'iyya mai nasara domin gujewa mayar da kasar hannun gurbatattun mutane, wadanda ba kishin kasar ba ne a zukatansu."

Buhari ya ce burin jam'iyyar adawa shine sayar da kadarorin da kasar ta mallaka tare da yin facaka da arzikin ma'adanan kasar, yana mai cewa yanzu kan Mage a kasar ya waye, babu wanda zai yarda karairayin jam'iyyar adawar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel