Yamutsi: Jami'an kwastam sun kama kwantenoni makare da kayan 'yan sanda gabanin zabe

Yamutsi: Jami'an kwastam sun kama kwantenoni makare da kayan 'yan sanda gabanin zabe

Yayin da ya rage saura 'yan kwanaki a gudanar da zabukan gama gari dake tafe, rundunar jami'an hukumar haka fasa-kwauri ta kwastam dake a shiyyar 'A' a Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke kwantenoni makare da kayan 'yan sanda da kuma barkonon tsohuwa.

Jami'an na hukumar Kwastam sun bayyana cewa dinkakkun kayayyakin 'yan sandan an kama su ne a daidai lokacin da ake kokarin batar da su a cikin kasar kan hanyar zuwa Legas cikin wata motar alfarma kirar Toyota Sienna.

Yamutsi: Jami'an kwastam sun kama kwantenoni makare da kayan 'yan sanda gabanin zabe

Yamutsi: Jami'an kwastam sun kama kwantenoni makare da kayan 'yan sanda gabanin zabe
Source: UGC

KU KARANTA: Tsohon dogarin Tinubu ya zama kwamashinan 'yan sanda a Kwara

Legit.ng Hausa ta samu cewa Kwanturolan shiyyar ta jami'an Kwastam wanda ya sanar da samun nasarar jami'an nashi mai suna FOU Muhammad Aliyu ya kuma shaidawa manema labarai cewa an cafke mutumin dake dakon kayan.

Haka zalika Mista Muhammad Aliyu ya sake bayyana cewa sauran kayayyakin da jami'an nasa suka kama a hannun bata-garin sun hada da barkonon tsohuwa, alamar matsayi, zariya, huluna da kuma ma katin shaida dukkanin su na 'yan sanda.

Ya kara da cewa suna zargin cewa wadanda suka shigo da kayayyakin na boge kuma harmtattu suna so ne suyi anfani da su wajen tafka ta'asa da laifuffuka a lokutan zabukan da ke tafe amma Allah ya kiyaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel