Sarauta cikin siyasa: Atiku ya samu saurautar Obong Emem na jihar Akwa Ibom

Sarauta cikin siyasa: Atiku ya samu saurautar Obong Emem na jihar Akwa Ibom

- A ranar Litinin, 28 ga watan Janairu, aka nada Atiku Abubakar a matsayin Obong Emem, a lokacin da ya je kaddamar da yakin zabensa a jihar Akwa Ibom

- Nadin sarautar ya gudana ne karkashin shugaban majalisar sarakuna ta jihar, Mai martaba Ntong Effiong Uduakpa, a madadin sauran masu rike da sarautun gargajiya

- Al'ummar jihar sun jinjinawa Atiku Abubakar, bisa ladabi da girmamawar da ya nunawa masarautun gargajiyarsu

Dan takar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, Alhaji Atiku Abubakar ya samu gagarumar tarba a fadar masarautar jihar Akwa Ibom, inda kuma har aka nada shi sarautar Obong Emem na Akwa Ibom.

A ranar Litinin, 28 ga watan Janairu, aka nada Atiku Abubakar a matsayin Obong Emem, a lokacin da ya je kaddamar da yakin zabensa a jihar Akwa Ibom, da nufin neman kuri'un jama'a da zai bashi damar zaman shugaban kasar Nigeria na gaba.

Nadin sarautar ya gudana ne karkashin shugaban majalisar sarakuna ta jihar, Mai martaba Ntong Effiong Uduakpa, babban basarake da ke a karamar hukumar Ini, a madadin sauran masu rike da sarautun gargajiya.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: IGP Adamu ya yiwa dukkanin mataimakan Sifeta Janar ritaya - Majiya

Sarauta cikin siyasa: Atiku ya samu saurautar Obong Emem na jihar Akwa Ibom
Sarauta cikin siyasa: Atiku ya samu saurautar Obong Emem na jihar Akwa Ibom
Asali: Facebook

Haka zalika dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar ta PDP, ya yi amfani da wannan damar wajen ganawa da shuwagabannin al'umma a jihar da kuma neman tubarrakinsu a yayin da kasar ke fuskantar zaben shugaban kasa a ranar 16 ga watan Fabreru.

Al'ummar jihar sun jinjinawa Atiku Abubakar, bisa ladabi da girmamawar da ya nunawa masarautun gargajiyarsu, a yayin ziyarar da ya kai ziyara ga majalisar sarakunan kasar lokacin da ya shiga jihar.;

Wannan ziyarar da Atiku ya kai jihar, ta yi sabani da ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar a makon da ya gabata.

Ziyarar shugaban kasa Buhari ta ci karo da wani taron al'ada da ake yi a jihar, na nadin sarautar Oku Ibom Ibibio, wanda kuma ya saba da tsarin jihar, la'akari da cewa kungiyar ci gaban jihar Akwa Ibom ALM ta aikewa APC sako kan wannan bukin nadin sarautar da zasu yi, amma APC bata mayar da hankali kan hakan ba, ta kaddamar da yakin zabenta a ranar, wanda ya jawo cece kuce a cikin jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel