Labarin hotunan yadda Sakkwatawa Shehu suka tarbi Buhari a filin Giginya
Mun kawo muku rahoton isar shugaba Muhammadu Buhari jihar Sokoto domin yakin neman zabensa karo na biyu. Jirgin shugaban kasa ya isa filin jirgin saman Sultan Abubakar ne misalin karfe 10:05.
Manyan jami'an gwamnatin jihar Sokoto sun tarbi shugaba Buhari yayinda ya da sauka. Daga cikin wadanda suka tarbesa sune gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon gwamnan jihar, Ahmad Sani Yarima; ministan harkokin mata, Aisha Abubakar da sauran manyan jiga-jigan jam'yyar APC.
Daga saukarsa, shugaban kasan ya garzaya fadar mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad, domin kai masa gaisuwar ban girma.
Kalli hotunan abinda ya auku:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng