Allah daya gari ban-bam: Rihanna ta maka mahaifinta kotu kan sanya sunansa a kasuwanci

Allah daya gari ban-bam: Rihanna ta maka mahaifinta kotu kan sanya sunansa a kasuwanci

- Mawakiya Rihanna ta maka mahaifinta Ronald Fenty kotu, bayan yayi amfani da sunansa a wata harkar kasuwanci

- Rihanna ta yi ikirarin cewa mahaifinta da abokin kasuwancinsa sun damfari mutane da cewar kamfaninsu mai suna Fenty Entertainment na aikine da izininta

- Mr. Fenty da abokin kasuwancinsa an sake zargin su da karbarwa Rihanna aiki na yin wasanni har a wurare 15 a Latin America akan kudi $15mln

Rihanna Fenty, shahararriyar mawakiyar kasar Amurka wacce aka fi sani da Rihanna, ta maka mahaifinta Ronald Fenty kotu, bayan yayi amfani da sunansa a wata harkar kasuwanci.

Rihanna tuni ta alkinta sunan 'Fenty' domin yin wani kasuwanci, sai dai mawakiyar tayi ikirarin cewa ta maka mahaifin nata kotu ne saboda yayi amfani da sunansa wajen yin wani kasuwancin alhalin tuni ita ta kuduri yin hakan.

A cewar wata takarda daga kotun wacce mujallar Amurka ta TMZ ta samu a ranar Talata, mawakiyar wacce ta shigar da karar a wata kotun gwamnatin tarayya da ke California, ta yi ikirarin cewa mahaifinta da abokin kasuwancinsa, Moses Joktan Poerkins "sun damfari mutane da yaudararsu da cewar kamfaninsu mai suna Fenty Entertainment na aikine da izininta."

KARANTA WANNAN: Saboda mutuwar dan majalisar tarayya: Majalisar dattijai ta dage zamanta na yau

Allah daya gari ban-bam: Rihanna ta maka mahaifinta kotu kan sanya sunansa a kasuwanci
Allah daya gari ban-bam: Rihanna ta maka mahaifinta kotu kan sanya sunansa a kasuwanci
Asali: Twitter

Da wannan ne mawakiyar ta yi ikirarin cewa a yunkurin da suka yi na cin riba da sunan, mahaifinta yayi yunkurin alkinta sunan 'Fety' da zummar kasuwanci da shi, alhalin tuni ta yi hakan.

Takardar da aka samu daga kotun ta kara bayyana cewa Mr Fenty "yayi amfani da karya da nufin damfarar wasu mutane miliyoyin daloli da yi masu alkawarin cewa suna aiki ne a madadin Rihanna, kuma da cewar Rihanna zata iya zuwa wasa a kowanne sashe na duniya."

Mr. Fenty da abokin kasuwancinsa an sake zargin su da karbarwa Rihanna aiki na yin wasanni har a wurare 15 a Latin America akan kudi $15mln.

Rihanna dai na bukatar kotu ta haramtawa mahaifinta amfani da sunan 'Fenty' wajen yin kasuwancinsa. Ta ce ba sau daya ba ba sau biyu ba, ta yi kokarin tuntubar mahaifin nata domin dorashi akan hanya, sai dai mahaifin nata yaki ya ji maganarta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng