Fasahar matasa: Wani hazikin matashi a Najeriya ya kera motoci da jirgin sama daga kananan karafa
Hakika babu ko shakka cewa kasar Najeriya cike take da matasa maza da mata masu dumbin fasaha a ko wane irin fannonin rayuwa daga garin Badagry a jihar Legas har zuwa garin Maiduguri a jihar Borno.
Haka zalika kamar dai yadda masu bibiyar mu suka saba gani, mukan zakulo maku wasu daga cikin matasan da suka yi wani abun a yaba ko ya baza hazakar sa domin duniya ta gani kuma watakila ma ya samu taimako daga gwamnati ko daidaikun mutane.

Asali: UGC
KU KARANTA: An nemi Buhari da Osinbajo a wajen muhawara
A yau ma dai muna dauke ne da labarin wani hazikin matashi mai suna Wisdom Ibeabuchi Eze da Allah ya yassarewa yin anfani da kananan karafa da kayan nauyi wajen kera samfurin motoci kala-kala da kuma jirage.
Tun bayan da hotunan kere-keren na matashin suka soma bayyana a kafafen sadarwar zamani dai, al'umma da dama suke ta tofa albarkacin bakunan su tare da sa masa albarka.
A hannu guda kuma wasu kira sukayi da gwamnatin tarayya da ma ta jihar da matashin ya fito da su taimaka masa musamman wajen ganin ya daukaka tare da cimma burin sa a rayuwa.
Ga dai wasu hotunan kere-keren matashin:
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng