Jawabin bankwana: Na cimma duk wani burina a aikin dansanda – Inji Tsohon sufeta janar
Tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris ya bayyana cewa lokaci ya yi daya kamata ya ja da baya ta hanyar yin ritaya daga aikin dansanda domin baiwa yan baya dama su bada irin tasu gudunmuwar wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban Najeriya gaba daya.
Idris ya bayyana haka ne a yayin da yake gabatar da jawabin ban kwana ga abokan aikinsa kafin taron mika ragamar iko ga sabon sufetan Yansandan Najeriya, Adamu Mohammed da za’ayi a ofishinsa dake shelkwatar Yansanda a Abuja a ranar Laraba.
KU KARANTA: Bikin tunawa da yan mazan jiya: Kalli yadda Buhari ya karrama Sojojin da suka mutu

Asali: Facebook
A jawabinsa, Idris yace a ranar Talata 15 ga watan Janairu ya cika shekaru sittin a rayuwa, duba da cewa an haifeshi ne a ranar 15 ga watan Janairun 1959, don haka ya cika sharadin ritaya daga aiki, bugu da kari ya cika shekaru 35 yana aiki, shima wani sharadi ne na ritaya.
Legit.ng ta ruwaito Idris yana cewa a shekaru 35 da yayi yana aikin dansandan ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare rayuka da dukiyan yan Najeriya, don haka lokaci yayi da zai ajiye aiki, ya fada wani sabon babi na rayuwar dan adam.
“Ina mika godiyata a gareku duka muka yi aiki tare, idan har na cutar daku, don Allah ku yafeni, nima kuma na yafe ma duk wanda na cuta, saninku ne wannan aikin namu yana da dan karan wahala, amma dole ne mu gode ma Allah daya kawo mu wannan matsayi a aikin Dansanda.
“Ina kira a gareku daku riki wannan sabon sufetan Yansanda a matsayin abokinku, kuma dan uwa, ina fata zaku bashi duk gudunmuwar data dace da shi.” Inji shi.
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da nadin AIG Adamu Mohammed a matsayin sabon babban sufetan Yansanda, Buhari ya sanar da haka ne bayan wata ganawa da yayi da Adamu da Sufeta mai barin gado Ibrahim Idris, inda suka kara ma Adamun girma.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng