Siyasar jihar Adamawa: Yan takaran gwamna 11 sun koma jam'iyyar APC

Siyasar jihar Adamawa: Yan takaran gwamna 11 sun koma jam'iyyar APC

Shugaba jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Adams Oshiomole, ya karbi yan takaran gwamnan jihar adamawa 11 daga jam'iyyu daban-daban da suka dawo jam'iyyar a ranan Talata, 8 ga watan Junairu, 2019.

Oshiomole ya ce bayyana cewa sauya sheka wadannan yan takaran zuwa APC na nuna cewa jam'iyyar zata samu nasara a zaben 2019.

Yace: "Ina matukar farin ciki da muku maraba zuwa jam'iyyar All Progressive Congress (APC). Dukkanku na da ikon zama gwamnoni, amma kuka zabi ajiye aniyarku domin taimakawa gwamna Bindow."

"A madadin shugaba Muhammadu Buhari, muna muku maraba kuma mun gode muku da amincewa da kukayi da APC,"

KU KARANTA: Daga karshe, hukumar Soji ta saki dan jaridan Daily Trust

Oshiomole ya yi kira ga jama'ar jihar su yunkura su karbi katin zabensu kuma su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaben APC a zaben bana.

Yan takaran jam'iyyun da suka sauya sheka sune na KOWA, PPN, AMP, PPA, YPP, NCP, AMP, MEGA PARTY, ZLP, APGA da UNPP.

Umar Jada, dan takaran jam'iyyar APGA wanda yayi magana a madadin sauran ya bayyana cewa sun yanke shawaran komawa APC ne saboda irin ayyukan da akayi a jihar da kasa ga baki daya.

Yayi a;kawain cewa dukkansu da mabiyansu za suyi aiki tukuru domin tabbatar da nasaran dukkan yan takaran APC a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel